1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na karuwa a yammacin Afirka ta Tsakyia

January 19, 2014

Fada na cigaba da wakana a Jamhuriya Afrika ta Tsakiya daidai lokacin da ake dab da bayyana wanda ke neman mukamin shugaban rikon kwaryar kasar.

https://p.dw.com/p/1AtOH
Hoto: Reuters

Yayin da ake dab bayyana jerin wadanda suka nuna sha'awarsu ta zamantowa shugaba na rikon kwarya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, rikici na cigaba da kankama a kasar.

Wani jami'in dakarun kasashen Afrika ta Misma da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ya shaida wa kamfanin dillancin labari na AFP cewa rikicin na karuwa a yammacin kasar musamman ma dai daura da kan iyakar kasar da Kamaru da kuma garin Sibtut da ke arewa da Bangui fadar gwamnatin kasar.

A ranar Asabar ma rahotanni sun ce an far wa wata mota kirar akori kura da ke dauke da wasu musulmi da suke kokarin yin gudun hijira inda aka jefa musu gurneti, batun da ya yi sanadiyyar rasuwar wasunsu ciki har da kanana yara.

Karuwar gwabza fadan da ake a kasar na cigaba da jawo nuna damuwa kan halin da al'ummar kasar musamman ma dai yara ke shiga sakamakon fadan, har ma kungiyar nan ta Save the Children da ke kare hakkin kananan yara ta ce ya kyautu a duba halin da yara ke ciki.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal