1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici na mamaye arawacin Najeriya

April 25, 2014

Gwamnatin Najeriya ta bayyana daukan matakan kubuto da 'yan matan da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su

https://p.dw.com/p/1Bofy
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Mahukuntan da ke ikirarin kai gwauro da mari da nufin nemo 'yan mata 'yan makaranta kusan 200 da wasu da ake jin 'yan Boko Haram ne suka sace, an shiga mako na biyu na batan 'yan matan tare da gwamnatin jihar na fadin har yanzu da sauran tafiya a tsakanin jami'an tsaron da gano yaran da batansu ke kara tada hankula ciki da wajen kasar.

Satar yaran kusan 200 daga wata makarantar 'yan mata a Garin Chibok da ke kudancin Jihar Borno dai ya zuwa yanzu ya zama daya a cikin manyan masu tada hankali na aiyukkan 'ya'yan kungiyar Boko Haram mai fafutuka da bama-bamai da kuma tasirinta ke ratsa ko'ina cikin kasar.

Abin kuma da ya kai ga talashin jami'an tsaron da a farkon fari suka ce sun kwato su har sun kama guda a cikin 'yan satar, kafin daga baya su sauya batu tare da amsa karatun har yanzu da sauran aiki.

Alhaji Kashim Shettima
Gwamnan Jihar Borno, Kashin ShettimaHoto: DW/U. Musa

Makonni biyu bayan nan dai har ya zuwa yanzu babu alamun fata a bangaren jami'an tsaron da ke ci gaba da lalube amma kuma babu duriyar yaran da aka sace suna karatun jarabawar karshe.

To sai dai kuma duk da hakan a fadar gwamna Kashim Shettima na Jihar ta Borno, gwamnatin jihar ta gamsu da jeri na matakai na jami'an tsaron da a cewarsa sun yi nisa a kokari na sake hade yaran da iyayensu.

“Yan matan, sojojinmu na iyakacin kokarinsu su ga cewar an ceto 'ya'yan nan namu amma kuma ban cancanta ko na san ina yaran suke in yi magana ba fisabillilahi.”

Tuni dai al'amura ke nuna alamun karin rudewa ga gwamnatin da ke fustantar bore na iyayen yaran da ke fadin hakuri ya kare kuma shiga daji da nufin gano 'ya'yansu na zaman mafitar karshen halin da ake ciki dai, abin kuma da farkon mako ya kai ga gwamnan zuwa garin na Chibok domin ban hakuri, a fadarsa ya kama hanyar tasiri ga kokari na kaucewar biyu babu a tsakanin 'ya'ya da iyayen da ke ganin an kasa. “Wannan mun ba su hakuri naje Chibok ni da kaina ranar Litini mun ba su hakuri kuma sun yi hakuri.”

To sai dai kuma a yayin da Jihar Borno ke can na lallashin mata da nufin hanasu tunkarar 'yan kungiyar Boko Haram dai, can a makwabciyarta ta Taraba in da a farkon makon aka kai ga kisan mutane sama da 30 a tsakanin garururwan Wukari da Ibbi, rikicin na kama da na masu neman kwatar mulki ko ta halin kaka a fadar gwamnan jihar dake riko Alhaji Garba Umar:

Nigeria Kampf gegen Boko Haram Islamisten
Hoto: Getty Images/AFP

“Mun ga wannan ba ainihin fadan addini ba ne fadan siyasa ne. mutane ne da ke ganin in ba sun zama gwamna ba to babu zaman lafiya. Ina ganin mutanen Taraba ya kamata su tashi tsaye su ga cewar duk mutumin da ke neman fitina ko ya kawo fitina bai kamata a zabe shi ba. Kuma a gefen fadan an yi kame-kame kuma yadda aka fahimtar dani shi ne har da ma uniform din soji.”

Abin jira a gani dai na zaman tasirin kokarin mahukuntan na tabbatar da karshen rigingimun da ke da salo daban-daban a wurare daban-daban amma kuma ke barazana ga makomar kasar da tai dari take kuma fatan damawa a kan gaba cikin wasu darin masu zuwa.

Mawallafi: Ubale Musa/Suleiman Babayo
Edita: Pinado Abdu Waba