1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici tsakanin makiyaya da manoma ya ki ci ya ki cinyewa

Mohammad Nasiru AwalApril 28, 2016

Har yanzu da jan aiki a gaba a kokarin da hukumomi da kungiyoyin farar hula ke yi don magance rigingimu tsakanin makiyaya da manoma.

https://p.dw.com/p/1Iee9
Kenia Rinderhüter und Rinder in Kajiado
Hoto: dapd

Rikici tsakanin Fulani makiyaya da manoma na cigaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi musamman a tarayyar Najeriya duk kuwa da matakan da mahukunta da ma kungiyoyi masu zaman kansu ke yi na kawo karshen sa. Sai dai duk haka ba a yi kasa a guiwa ba wajen gano mafita daga rikicin na tsawon shekaru.