1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici ya sake barkewa a Mali

January 8, 2013

'Yan tawayen Mali na ci gaba da karbe iko da yankunan da ke karkashin ikon gwamnati yayin da Burkina Faso ke shirya taron neman maslaha ga rikicin.

https://p.dw.com/p/17FhQ
Militiaman from the Ansar Dine Islamic group sit on a vehicle in Gao in northeastern Mali in this June 18, 2012 file photo. To match Special Report MALI-CRISIS/CRIME REUTERS/Adama Diarra/Files (MALI - Tags: CIVIL UNREST CRIME LAW POLITICS RELIGION)
Hoto: REUTERS

Wani jami'in sojin Mali ya sanar da cewar 'yan tawayen da ke da iko da rabin kasar, wadanda ke gudanar da harkokin mulki a yankin arewaci, na nausawa zuwa yankunan da ke karkashin ikon gwamnati a yankin kudancin kasar ta Mali. Jami'in, wanda ya bukaci a sakaya sunansa domin ba a bashi umarnin yin jawabi ga kafofin yada labarai ba, ya ce tun da yammacin wannan Litinin ne 'yan tawayen suka isa kauyen Bourei, mai tazarar kilomita 40 kachal daga gari na karshen da ke hannun sojojin gwamnati a yankin.

Ci gaba da nausaawar da 'yan tawayen ke yi dai na tada fargabar cewar mayakan da ke da ala'ka da kungiyar al-Qa'ida za su iya kwace wasu yankunan da ke kudancin kasar. Kazalika, wannan matakin na zuwa ne a dai dai lokacin da sassan da lamarin ya shafa ke shirye shiryen gudanar da tattaunawar neman kawo karshen rikicin arewacin kasar a kasar Burkina Faso.

Idan za a iya tunawa dai tun cikin watan Afrilun bara ne gwamnatin Mali ta rasa iko a yankin arewacin kasar, inda daga baya kuma kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya bayar da umarnin daukar matakin soji - a kokarin kwato yankin daga hannun 'yan tawayen.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe