1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Biafra ya janyo martanin kungiyoyi

Uwais Abubakar IdrisMay 31, 2016

Kungiyoyin kare hakin jama’a zasu shigar da kara a kotun kasa da kasa a kan amfani da karfi da kisan masu zanga-zangar tuna ranar Biafra da jami’an tsaron Najeriya suka yi

https://p.dw.com/p/1Ixm4
Demonstration für politischen Aktivisten Nwannekaenyi Nnamdi Kenny Okwu Kanu
Hoto: picture alliance/NurPhoto

Kungiyoyin kare hakin jama'a na Najeriyar da ma kasa da kasa na cigaba da nuna rashin jin dadinsu har ma da masu yin tir da abin da suka kira karuwar amfani da karfi da ya wuce kima har ma da makamai a kan masu rajin kafa kasar Biafra, wanda suka ce ya sabawa dokoki na kasa da kasa da Najeriyar ta sanya hannu musamman a matsayinta na kasa mai bin tafarkin demokrardiyya.

Kungiyar marubuta batutuwan da suka shafi kare hakin jama'a da ta ce a kan idon wakilan da ta tura aka yi dauki ba dadi a jihohi da daman a ‘yan kabilar Igbo da suka yi bikin cika shekaru 49 da zagayowar ranar Biafra, ta ce zasu nufi kotun kasa da kasa ta ICC domin tilastawa jami'an tsaron Najeriya bayyana dalilin kisan da take zargin sun aikata. Mr Emmanuel Nwobiko shine shugaban kungiyar.

Demonstration für politischen Aktivisten Nwannekaenyi Nnamdi Kenny Okwu Kanu
Hoto: Getty Images/AFP/P.U. Ekpei

Tuni dai kungiyoyin kare hakin jama'a na kasa da kasa da ke Najeriyar na Amnesty International da Human Rights Watch suka ce suna nazari da ma bincike abinda ke faruwa domin daukan matakin da ya dace. Koda na tuntubi Mausi Segun ta kungiyar Human Rights Watch ta ce, da zarar sun kammala bincikensu zasu fitar da matsayinsu.

Har zuwa wannan lokaci dai babu cikakken adadin yawan mutanen da aka kashe a arangamar da ta shafi jihohi shida na Kudu maso Gabashi da kudncin Najeriyar da suka hada da Ebugu, Ebonyi, Abia da Delta. Sai dai a Onisha ne abin yafi muni saboda zargin afkawa masu zanga-zangar.