1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Boko Haram da na 'yan tawaye a Mali

Mohammad Nasiru AwalMarch 13, 2015

A wannan makon jaridun sun mayar da hankali a kan Najeriya bayan shelar yin mubaya’a ga kungiyar IS da Haram Abubakar Shekau ya yi.

https://p.dw.com/p/1EqTE
Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

A wani labari mai taken fagen daga a Afirka jaridar Der Tagesspiegel ta fara ne da cewa bisa ga dukkan alamu matakan soji na hadin guiwa da kasashe hudu na yammacin Afirka ke dauka kan mayakan Boko Haram ya fara yin tasiri. Bayan da Boko Haram ta fadada hare-hare a ilahirin yankin da ke kewayen tafkin Chadi, kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru sun hada karfin sojojinsu wajen mayar da martani. Ya zuwa tsakiyar wannan mako sojojin kawance sun sake kwato garuruwa kimanin 36 daga hannun mayakan Boko Haram. Watakila saboda wannan matsin da yake fuskanta Abubakar Shekau ya nuna yin mubaya'a ga kungiyar IS. Da wuya a iya fassara wannan mubaya'a amma rundunar sojin Najeriya ta ce alama ce ta rauni wadda kuma ke nuni da samun nasarar matakan sojin da ake dauka kan masu ta da kayar bayan.

Yaki da Boko Haram don kare muradun kai

Da gaske kasar Chadi take a yakin da take yi da Boko Haram inji jaridar Neue Zürcher Zeitung.

Tschad Armee Boko Haram
Sojojin Chadi a filin dagaHoto: Reuters/E. Braun

Jaridar ta ce baya ga mafaka da gwamnatin Chadin ta ba wa dubbannen mutanen da suka tsere daga rikicin Boko Haram a yankin da ke kan iyaka da Najeriya, sojojin Chadin da suka kware a yakin basasa, sun nuna bajimta idan aka kwatanta da dakarun Najeriya da suka fi kayan yaki, a fadan da ake yi da Bokon Haram. Sojojin Chadi da ake wa lakabi da mayakan hamada tun a cikin watan Janeru sun kwato garuruwa da dama da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya. To sai dai a cewar jaridar kutsen da Chadin ke yi na da wani maradi na radin kai, domin hare-haren da Boko Haram ke kaiwa na barazana ga man da Cahdin ke turawa ketare sannan yana cikas ga harkokin ciniki.

Fatan samun zaman lafiya a Mali ya ragu

Daga rikicin Boko Haram a Najeriya sai na ‘yan tawaye a kasar Mali, inda jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce har yanzu Mali ba ta samu kwanciyar hankali ba.

Mali Anschlag auf ein Restaurant in Bamako
Binciken ababan hawa a Bamako bayan hari a kan gidan rawaHoto: AFP/Getty Images/H. Kouyate

Ta ce hare-hare guda biyu a kasar daya a birnin Bamako daya kuma a kan sansanin sojojin Majalisar Dinkin Duniya a garin Kidal sun dakushe fatan samun zaman lafiya nan kusa a Mali. An shiga wannan zaman zullumi na baya-bayan nan biyo bayan kammala wani zaman taron tattauna batun samar da zaman lafiya da aka shafe tsawon lokaci ana yi a kasar Aljeriya tsakanin gwamnati da wakilan kungiyoyin ‘yan tawaye ba tare da wani sakamako na a zo a gano ba. Duk da cewa an amince da wata yarjejeniya a kan ba wa arewacin kasar jerin ‘yancin cin gashin kai idan suka amince a sake tsugunar da sojoji, amma shugabannin Abzinawa sun ki rattaba hannu kan yarjejeniyar har sai sun tuntubi magoya bayansu.

Shekaru 20 a gidan kaso

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tsokaci ta yi a kan hukuncin daurin shekaru 20 da wata kotu a kasar Cote d'ivoire ta yanke wa Simone Gbagbo matar tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo.

Ta ce Simone Gbagbo da a ranar Talata kotu ta same ta da laifin yin katsalanda a harkokin mulkin kasa da taka rawa a rikicin basasa da kuma hannu wajen ta da fitina, an yanke mata hukun cin daurin shekaru 20 a kurkuku. An kuma same ta da laifin kafa kungiyoyin masu kisa da suka aikata ta'asa a yakin basasan kasar a sherkarun 2002 zuwa 2007.