1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Burundi ya sa al'umma tserewa

Pinado Abdu WabaApril 16, 2015

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa dangane da abin da ke faruwa a Burundi domin ya tilastawa fararen hula barin matsugunnensu

https://p.dw.com/p/1F9Vb
Burundis Präsident Pierre Nkurunziza
Hoto: F. Guillot/AFP/GettyImages

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya bayyana damuwarsa dangane da rahotannin tashe-tashen hankulan da ake samu daga Burundi gab da za a yi zaben shugaban kasa, ya kuma yi kira ga jagororin kasar da su tabbatar an yi zabe mai tsabta.

Batun cewa mai yiwuwa shugaba Pierre Nkurunziza ya nemi wa'adi na uku - duk da cewa bai riga ya bayyana wannan kudurin a hukumance ba- ya janyo rikicin da ake kwatantawa a matsayin mafi muni tun bayan yakin basasar kasar na shekaru 12, wanda aka gama a shekara ta 2005. Yanzu da dai 'yan kasar da dama sun tsere zuwa makwabciyarsu Ruwanda domin samun mafaka