1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin cikin gida a jam'iyyar PNDS Tarayya a Nijar

Mahaman Kanta/ MNAAugust 26, 2015

Jam'iyyar PNDS Tarayya da ke mulki a Nijar ta kori Ibrahim Yakuba, mataimakin darakta a fadar shugaban kasa, bayan da wasu kusoshin jam'iyyar suka ga zai bata musu haraka.

https://p.dw.com/p/1GMZW
Niger Präsident Mahamadou Issoufou
Hoto: DW/M. Kanta

Ko da yake ba da dade wa ba ne dai Ibrahima Yakuba ya shiga jam'iyyar ta PNDS Tarayya da ke mulki a Nijar, amma tauraronsa ke haskakawa musamman tsakanin matasa, abin da wasu tsoffin kusoshin jam'iyyar ke ganin tamkar barazana ne gare su.

A gun wani taron gaggawa da Kwamitin zartarwa na kolin ya kira ya ba da sanawar korar Mallam Yakuba da ke zama mataimakin daraktan jam'iyyar a fadar shugaban kasa.

Honorable Zakari Oumaru memba ne a Kwamitin zartarwar PNDS tarayya shi ne ya karanta takardar korar Ibrahim Yakuba.

"Kamar yadda kuka sani jam'iyyarmu ta PNDS Tarayya ta fuskanci wasu matsaloli a cikin gudunmar Dogon Dutse. Sanadinsu shi ne shigowar Ibrahima Yakuba mataimakin darakta a fadar shugaban kasa. Ya zo Dogon Dutse ya shiga cikin jam'iyya, shigar da ya yi cikiin jam'iyya ita ce ta haddasa fitina da ta yi dalilin wannan sanarwa."

Niger Niamey Opposition
'Yan adawa a Nijar ma na fama da rikicin cikin gidaHoto: DW/M. Kanta

Shugaban koli na jam'iyyar sun zarge shi da rashin ladabi da furta kalaman ta da fitina.

Take-taken da suka saba wa tsarin mulki

Wasu abubuwan ma a cewar Zakari Oumaru sun haramta karkashin kundin tsarin mulkin kasa da kuma dokokin jam'iyya. Saboda haka jam'iyyar ta dauki matakin koras daga cikinta.

Da farko dai Ibrahim Yakuba ya yi alkawarin mayar da martani amma kuma ya fasa.

Wannan takaddama a cikin jam'iyyar PNDS Tarayya ta zo ne yayin da ake tinkarar zaben shekarar 2016 a Nijar, lokacin da jam'iyyar ke matukar bukatar yawan magoya baya.