1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba tsakanin Falasdinu da Isra'ila

Mahmud Yaya Azare / LMJOctober 16, 2015

Duk da matsanancin matakan tsaron da Isra'ila ta dauka a yankunanta dama yankunan Falasdinawa, dubban Falasdinawan sun bazama kan tituna a ranar da suka kira da "Ranar Fushi".

https://p.dw.com/p/1Gpa0
falasdinawa na ci gaba da zanga-zanga
falasdinawa na ci gaba da zanga-zangaHoto: picture-alliance/AP Photo/M. Illean

Kama daga Ramallah da Birnin Kudus har zuwa Zirin Gaza, dubun-dubatar Falasdinawan da ke fushi da Isra'ila ne sukai tattaki kan tituna suna rera taken nuna kyama ga abin da suka kira "Cin zali marar iyaka na Isra'ila da kokarin sauya fasalin masallacin Al'Aksa, dangane da wuraren yin ibada a cikinsa da kuma lokotan yin ibadar.

Falasdinawa na nuna fushinsu

Hassan Yusuf kusa a kungiyar Jihadul Islami ya ce yanzu babu wani sauran banbance-banbancen siyasa tsakanin al'ummar Falasdinawa wajen tunkarar shirin da Isra'ila ke aiwatarwa na ganin bayan al'ummarsu inda ya ce zanga zangar da suke yi ta nuna fushinsu ne ga irin halin mamayar da suke fuskanta daga Isra'ila wanda ya zamo wajibi su nuna mata ba fa ita kadai ce a duniya ba.

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas
Shugaban Falasdinawa Mahmud AbbasHoto: Reuters
Halin da mata da kananan yara kan tsinci kansu a ciki.
Halin da mata da kananan yara kan tsinci kansu a ciki.Hoto: Getty Images/AFP

Goyon bayan gwagwarmayar lumana

Shima kansa shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, wanda wasu ke zargin sa da mika wa Isra'ilan wuya bori ya hau, ya ce shima yana goyan bayan gwagwarmar lumanan da al'ummar Falalsdinawa ke yi don kwato hakkinsu. Ya kara da cewa za su ci gaba da yin gwagwarmaya ta hanyar tattaki a kan tituna kamar yadda za su ci gaba da yi a zaurukan Majalisar Dinkin Duniya da tarukan kasa da kasa har sai sunga bayan abin da ya kira da mulkin mallaka daya tilo mafi tsayi da ya rage a doran kasa.