1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

RIKICIN IRAKI.

Zainab Mohammed.November 12, 2004
https://p.dw.com/p/Bvef
Fallujah Iraki.
Fallujah Iraki.Hoto: AP

Da yammacin yau ne dakarun Amurka suka sanar da gano wani kurkukun karkashin kasa ,dauke da gawawwakin mutane biyu da kuma wasu biyu da wasu wa da kani dake raye a garin Fallujah.An dai gano wannan kurkukun ne a a wani gida dake wani yanki da ake kira Jolan,inda kuma ake zargi da kasancewa wurin mafakan yan yakin sunkurun na Fallujah.

Wani mai daukan hoton kamfanin dillancin labaru na AFP daya shiga wannan gida yayi bayanin cewa,yaga gawwakin mutane biyu rufe da toka,ayayinda wasu mutane biyu kuma suna zaune tamkar mahaukata a kusa da gawawwakin dake wannan gidan kurkuku na karkashin kasa,inda daga baya ne Amurkawan suka tafi dasu.

Tun a ranar litinin nedai dakarun Amurka dana Iraki suka kutsa garin na falluja dake dauke da yan tawaye,da nufin fatattakansu,gabannin zaben wannan kasa da zai gudana a watan janairu idan mai duka ya kaimu.

Da farkon kutsawansu a yammacin litinin dai,sunyi tsammanin kammalawa da yakin sari ka noken cin lokaci kalilan,amma daga baya suka lura dacewa abokan adawan nasu basa shirin tsagaita wuta balle mika wuya a wannan fafatawa da sukeyi da juna.Bayan nan ne dakarun Amurka dana Irakin suka fara kutsawa gidajen da suke zargi ana mayar musu martanin hare haren da suke kaiwa.

A hannu guda kuma acigaba da sace sacen mutane domin garkuwa dasu a kasar ta Iraki,daga watan Afrilu zuwa yanzu kimanin yan kasashen waje dake aiki a kasar 200 aka ,kungiyoyin yan yakin sunkurun daban daban sukayi garkuwa dasu.To sai dai yan kasar ta Iraki suma kann fuskanci ire iren wannan barazana.

A yau din ne kuma wata mai magana da yawun sojin Amurkan ta sanar dacewa sun gano wani Direba dan kasar Syria da aka sacesu tare da yan jaridan nan biyu na kasar faransa,kusan watanni 3 da suka gabata a Irakin.

Acan kudancin Falluja kuwa ana cigaba da dauki ba dadi tsakanin sojin Amurkan da yan yakin sunkurun,wanda ke neman kawo cikas cikin harkoki na agajin abinci da magunguna da ake kokarin shigarwa alummar wannan yanki.

A dangane da hakane ma kungiyar agajin ta kasa da kasa ta red cross tayi kira ga bangarorin biyu dasu tsagaita wuta,domin basu daman shigar da wadannan kayyaki na agaji.

Acan garin dake areci kuwa wasu yan yakin sari ka noke sun kai hare haren boma bomai,a kwanaki biyu da suka gabata,koda yake rikicin ya samu lafawa a yau,

To sai dai dakarun Amurka na ganin cewa wanda suke nema ,kuma suke zargi da kasancewa jagoran haren kunar bakin wake da ake afka musu da ita watau Abu Musab al-Zarqawi,ya fice daga garin na falluja kafin kutsawarsu ranar litinin da yammaci.