1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Isra'ila da Falisdinawa ya kama hanyar rincabewa

November 15, 2012

Komitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya(MDD) ya ba da shawarar gudanar da tattaunwar gaggawa akan halin da ke wakana a yankin Gabas ta Tsakiya

https://p.dw.com/p/16jV9
Palestinian youths evacuate an elderly man following an Israeli air strike on November 14, 2012 in Gaza City. A top Hamas commander was among seven people killed in more than 20 Israeli air strikes on the Gaza Strip, as Israel began an operation targeting militant groups. AFP PHOTO/MOHAMMED ABED (Photo credit should read MOHAMMED ABED/AFP/Getty Images)
Hoto: MOHAMMED ABED/AFP/Getty Images

Babban sakataren MDD, Ban Ki Moon ya yi kashedi game da barkewar sabon yakin Gaza. Jami'an majalisar sun ce akwai bukatar daukar mataki na bai daya a komitin sulhu tare da kiran halin da ke wakana a yankin Gabas ta Tsakiya tamkar wata barazana. Shugaba Obama ya ce Isra'ila tana da ikon kare kanta, ya kuma tuntubi firainstan Benjamin Netanyahu ta waya inda ya yi masa alkawarin ba shi goyon baya. Su dai shugabannin biyu sun daidata kan cewa wajibi ne Hamas ta daina kai hare-haren rokoki cikin Israila. Kasar Masar ta janye jakadanta daga Isra'ila ta kuma yi kira ga Jakadan Isra'ila da ke birnin Alkahira da ya bayyana a gaban ma'aikatan cikin gidan kasar. Wani mai magana da yawon shugaba Muhammed Mursi ya kira hare-haren tamkar na taadanci damutane da dama suka yi mutuwar shahada a cikinsu.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman