1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin jihar Borno na ci gaba da rutsawa da jami'an tsaro

February 19, 2014

Soja guda ya mutu sakamakon harin da mayaka suka kai a gidan wani tsohon janar a Maidugurin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1BBlh
Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

Jami'an 'yan sanda da ke Maidugurin jihar Bornon Najeriya sun sanar da cewar, wani harin da ake dangantawa da 'yan kungiyar nan da aka fi sani da suna Boko Haramun, da ya wakana a gidan wani tsohon janar na sojin kasar cikin dare, ya janyo mutuwar mutum guda. Kwamishinan 'yan sanda a jihar ta Borno, Lawan Tanko, wanda ya sanar da hakan, ya kara da cewar, janar Umar Tukur Buratai, ba ya cikin gidan nasa yayin da maharan suka kai wannan farmakin. Sai dai kuma ya kara da cewar, sojojin da ke gadin gidan, sun yi nasarar dakile yunkurin da maharan suka yi, wanda suka ce ya taimaka wajen saukaka ta'asar da harin ya janyo, amma kuma ya tabbatar da cewar soji guda ya mutu. Ko da shike kwamishinan 'yan sandan ya tabbatar da kai wasu hare hare a karamar hukumar Bama da ke jihar ta Borno, amma kuma bai yi wani karin bayani ba. Wadannan hare haren na zuwa ne kwanaki kalilan bayan wasu hare haren sun janyo mutuwar fiye da mutane 150 a jihohin Borno da Adamawa da ke makwabtaka da juna.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar