1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Kenya ya mamaye jaridun Jamus

Zainab Mohammed Abubakar
November 3, 2017

Jaridun Jamus sun tabo rikicin siyasar kasar Kenya inda aka samu gudanar da zaben shugaban kasa karo na biyu a ranar 26 ga watan Oktoba. Sannan ba su manta da rikicin Sudan ta Kudu ba.

https://p.dw.com/p/2myRA
Kenia Präsidentschaftswahl Wahlsieger Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters/T. Mukoya

A labarin da ta rubuta mai taken " Kasar da ta dare gida biyu" jaridar Berliner Zeitung, ta ce madugun adawa ya yi watsi da sakamakon zaben da ya bai wa Uhuru Kenyata nasarar zabe, Duk da sake zabensa da al'ummar Kenya suka yi a karo na biyu, shi kansa shugaba Kenyatta bai san inda rikicin wannan kasa da ke yankin gabashin Afirka zai kai ba.

Madugun adawa Raila Odinga da ya kaurace wa takarar zaben da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata, ya  yi kira ga jama'a da su nuna turjiya da gudanar da gangamin lumana domin nuna adawa da sakamakon zaben. A cewar mai shekaru 72 da haihuwar, idan babu adalci wa mutane, to ita ma gwamnati ta yi sallama da zaman lafiya.

A taron manema labaru da ya yi a Nairobi ranar Talata, duk da cewar madugun adawan Kenyan bai fada kai tsaye cewa mutane su fito su yi boren adawa da sakamakon zaben ba, watakila saboda gudun maimaicin halin da kasar ta tsicin kanta a ciki a shekaru 10 da suka gabata. A wani mataki na nuna rashin halarcin gwamnatin Uhuru Kenyata, Odinga ya nuna muradin kafa majalisar al'umma.

Rikcin Sudan ta Kudu ya dauki hankali

Rebellen in Südsudan
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Ita kuwa jaridar der Freitag sharhi yi mai taken " a daidai lokacin da Sudan ta Kudu ke fuskantar zubar da jini, Yuganda ta jaddada goyon baynta ga 'yan gudun hijira. Shin me hakan ya ke nufi?

Jaridar ta yi nazarin labarin Saveri Obama mai shekaru 23 da haihuwa kuma dan gudun hijira da ya tsere wa yakin da yaki ci yaki cinyewa a kasar Sudan ta Kudu. Yanzu misalin karfe 10 na safiya ce, a wannan kauye da ke kan iyakar Yuganda da kasarsa da ya baro a baya, amma tsananin yanayi na zafi ya kai wajen maki 40.

A karon farko wata matashiya mai aiki da kungiya mai zaman kanta, ta gabatar wa Saveri wani dan fili mai ciyayi a matsayin sabon matsuguninsa. Ya sauka kan gwiwarsa kana ya yi murmushi, wanda bai yi ba tsawon kwanaki. Ya bukaci samun ruwan sha. Amma aka ce masa ya yi hakuri, motar da ke kawo ruwan sha ya makale cikin tabo a sabuwar hanyar da ke zuwa Omogu, sabon sansanin 'yan gudun hijirar da Yuganda ta budewa matasa da ke fitowa daga Sudan ta Kudu.

Afrika Mosambik illegale Extraktion
Hoto: DW/M. Mueia

Sharhi kan kare muhalli a Afirka

"Rayuwar samar da sauyi" wannan shi ne taken labarin da jaridar Die Zeit ta rubuta dangane da wani matashi mai fafutukar kare muhalli da ya dukufa wajen wayerwa da 'yan uwanshi matasa kai dangane da shugabanni masu cin hanci da rashawa.

Miguel de Barros mai shekaru 37 da haihuwa a garin Gabus da ke yankin kudu maso yammacin  kasar Guinea Bissau, ya kafa wata kungiya mai membobin matasa sama da 100, wadanda ke fafutukar ganin cewar sun ceto garin nasu wanda shi ne mafi talauci  a yankin, tare da nuna musu illar kasancewar kasar dandalin safarar faudar ibilisi ga kudancin Amirka da Turai.