1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin makiyaya da manoma a Nijar

Larwana Malam HamiNovember 19, 2014

A yayin da makiyaya suka fara saukowa daga filayen kiwo zuwa cikin gonaki a dai dai lokacin da manoma ke cikin tattarar amfanin gona hankalin manoma ya tashi matuka

https://p.dw.com/p/1Dq3B
Niger Normaden Fulani Scharfherde bei Gadabeji
Hoto: AP

Wasu manoman dai sukan tashi a tar babu biyo bayan mamayar da makiyayan suka yi wa gonakin nasu, don haka a yanzu tuni jijiyoyin wuya suka fara tashi, inda hakan ya kai ga samun asarar rayuka. To sai dai ga kungiyar makiyaya ta kasa ta dora laifi ga wuyan hukumomi.


Hakikan a dai dai lokacin da a jamhuriyar Nijar a ko wace shekara manoma ke fara tattarar amfanin gona ne dai, hukumomi ke ruwa da tsaki wajen daukan matakan rigakafin fadace-adacen dake aukuwa a tsakanin manoma da kuma makiyaya inda hukumomi ke tsaida lokacin sakin gonakai ga makiyaya. To sai dai a bana tuni wasu manoman suka tashi a tutar babu a sakamakon mamayar da
makiyayan suka yi wa gonakin su inda suke bayyana takaicin game da wanan matsala ta zuwan makiyaya tun kafin cikar wa'adin da hukumar ta tsaida. Souleymane Yahaya yana daga cikin, wanda ya kwashe tsawon lokaci yana shiga tsakanin manoma da makiyaya a kasar, don ganin ba a kai ga bai hamata iska ba.

Burundi Landwirtschaft
Hoto: picture alliance/africamediaonline

A makon da ya gabata ma dai a garin dan Tumi dake cikin
karamar hukumar Alela an yi dauki ba dadi tsakanin manoma da makiyaya wanda ya ritsa da rayukan mutane guda goma da suka hada da manoma hudu da makiyaya shidda, kana kuma mutane 21 suka ji munanan raunuka.

A young fulani herdsmen
Hoto: DW

To amma a nasu bangaren kungiyar makiyaya ta kasa ta bakin shugaban ta Suleymane Gurgudu, ya dora laifi a wuyan magabata. A yanzu haka dai ana iya cewar salon aikace-aikacen tattarar amfanin gona ya canza daga bangaren manoma domin wata cimakar ma ba ta kai ga nuna ba suke fidda ita, don gudun zuwan makiyaya.

To amman a hanu daya jama'a na kokawa da manoman karkara da ke janyo barna dakansu a sakamakon daure nasu bisashen a bakin gida a wani mataki na gugar zana ga makiyaya.