1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin man fetur ya sa fira ministan Libiya barin aiki

March 11, 2014

Majalisar dokokin Libiya ta sallami fira ministan kasar bayan nasarar da 'yan tawaye suka yi wajen fara safarar mai zuwa ketare.

https://p.dw.com/p/1BNbU
Ali Seidan Ministerpräsident Libyen PK
Hoto: Reuters

Majalisar dokokin Libiya ta kori fira ministan kasar Ali Zeidan, bayan wata tankar da ke dauke da man fetur ta yi nasarar tserewa daga kasar - duk da tsaron da dakarun ruwan kasar ke bai wa tashoshin jiragen ruwa. Kakakin majalisar dokokin kasar Omar Hmeidan, ya shaida wa manema labarai cewar, a yanzu ministan kula da harkokin tsaron kasar Abdallah al-Thinni, shi ne zai kasance mukaddashin fira ministan. Wannan sabon labarin dai ya dagula rigingimun siyasar da kasar ke fama dasu, wadda kuma ke zama mamba a kungiyar kasashen da ke safarar man fetur zuwa ketare ta OPEC, inda hukumomi ke fafutukar mayar da bin doka da oda da kuma shawo kan kungiyoyin mayakan sa kai da suka taka rawa wajen kawar da mulkin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, wadanda a yanzu ke neman kaucewa bin doka da oda. A wannan Litinin ne dama fira minista Ali Zeidan ya shaida wa mambobin majalisar dokokin cewar, sojojin ruwan kasar na rakiyar tankar man fetur da 'yan tawaye suka cika, zuwa tashar ruwan da ke yammacin kasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Pinado Abdu Waba