1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Nuklear Korea ta Arewa

January 20, 2007
https://p.dw.com/p/BuTy

Wakilin Amurka a Koriya ta Arewa Christopher Hill ya ce gwamnati a fadar mulki ta Pyaongyang ta amince da ta sake komawa zaurin shawarwarin sassa shida akan shirinta na makaman nukiliya a cikin gaggawa. Hill yayi wannan bayanin ne bayan ganawa da takwaransa na kasar Japan a birnin Tokyo, zangonsa na biyu a bulaguronsa ga kasashen Asiya. Hill ya ce shawarwarin da aka gudanar baya-bayan nan tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa a birnin Berlin sun taimaka aka shimfida wasu manufofin da za a tattauna kansu nan gaba a kasar China. Bayan taron na Berlin dai Koriya ta Arewa ta ce ta cimma wata yarjejeniya da kasar Amurka ba tare da wani karin bayani ba.