1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Siriya na bazuwa ga maƙobta

Usman ShehuNovember 12, 2012

Dakarun gwamnatin Siriya na kai farmaki kan tungar 'yan tawaye a kan iyakokin ta da Turkiya da Isara'ila

https://p.dw.com/p/16hJ8
U.N. peace keepers on the Golan heights, between Syrian villages and those occupied by Israel, as seen on September 20, 2005. Syria is under heavy pressure from the U.S. for its support to Iraqi insurgents as well as a possible role in the assassination of former Lebanese Prime Minister Rafiq Hariri. Photo by Ammar Abd Rabbo/ABACAPRESS.COM +++(c) dpa - Report+++
Dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD a kan iyakar Siriya da Isra'ila a yakin GolanHoto: picture-alliance/dpa

Jiragen yaƙin gwamnatin Siriya sun tsaurara hare-hare kan ma buyar yan tawaye dake iyakar ƙasar da ƙasashen Turkiya da Isra'ila. Wani harin da dakarun gwamnatin Siriya suka kai a kan mafakar yan tawaye a kusa da iyakarsu da Turkiya, ta firgeta jama'a da yawa, inda a can kan iyakarsu da Isra'ila, nan ma Siriya ta cilla makamai kan inda yan tawaye suka kafa sansani. Ko da a ranar lahdi ma, sanda wata rokar da Siriya ta cilla ya shiga cikin yakin tuddan Golan wanda Isar'ila ta mamaye tun yaƙin shekara 1973, abinda ma ya sa a karo na farko Isra'ilan ta yi harbin gargadi cikin Siriya. Sakatare janar na MDD Ban Ki-moon ya bayyana damuwa kan yadda yaƙin na Siriya ke ƙara bazuwa, inda ya yi ƙira da a mai da suciya nesa. Yan tawayen Siriya da suka yi sansani a kusa da tuddan Golan sun yi ƙazamin karawa da sojan gwamnatin Siriya a ranar Lahdin da ya gabata. Shi kuwa magajin garin Cailapinar dake iyaka da Siriya ta ƙasar Turkiya, yace bama baman da jiragen yaƙin Siriya suka cilla, ya hallaka mutane aƙalla 20 yayin da wasu da dama suka jikkata.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Yahouza Sadissou Madobi