1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasa a Cote d´Ivoire

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Buml

Kawacance jam´iyun adawa a kasar Cote d´Ivoire sun maida martani ga kalamomin shigaban kasar Lauran Bagbo na zaman kan karagar mulki bayan 31 ga watann oktober muddun ba a shirya zaben shugaban kasa ba.

Kakakin jam´iyun Alphonse Djedje Mady, ya ce sam adawa ta yi watsi da wannan batu, ta yi tur da Allah wadai ga aniyar Lauran Bagbo ta yin kafar angulu, ga shirya zabe da nufin ya dawwama akan kujera mulki.

Tun dai makon da ya wuce, idan ba a manta ba, yan tawayen Cote d´Ivoire, wanda ke rike da arewancin kasar, su ka bayana kin amincewa da kasancewar Lauran Bagbo a matsayin shugaban kasa bayan 31 ga watan Oktober.

A shekara da ta gabata ne, Majalisar Dinkin Dunia, ta tsawaita wa´danin mulkin sa, da shekara daya, tare da kyautata zaton, a cikin wannan lokaci za a shirya zaben shugaban kasa, to saidai bisa dukan alamu, hakan ba zata samu ba, ta la´akari da, gagaramin jinkiri, da kuma tafiyar haiwainiyar da ake fuskanta, wajen shirya zaben.