1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Guguwar sauyi tana kara kadawa a Aljeriya

Mouhamadou Awal Balarabe SB
March 19, 2019

Matsayin manyan kasashe kan rikicin siyasa da ke barazana ga Shugaba Abdelaziz Boutefika na Aljeriya. Yayin da mataimakin-Firaminista ke Rasha da Chaina da Jamus kan mafita ga guguwar sauyi da ta kada.

https://p.dw.com/p/3FJu0
Algerien Algeir - Proteste gegen Abdelaziz Bouteflika
Hoto: Reuters/Z. Bensemra

Gwamnatin Aljeriya na neman shawo kawunan manyan kasashen duniya don su ba da hadin kai  ga yunkurin Shugaba Abdelaziz Boutefika na tsawaita wa‘adin mukinsa da nufin gano bakin zaren warware rikicin siyasa da ake fama da shi a kasar. Saboda haka ne mataimakin-Firaminista Ramtane Lamamra ya fara ya da zango a Rasha a kan hanyarsa ta zuwa Italiya da Jamus da Chaina.

Wasu daga cikin shugabannin adawa sun yi na’am da wannan mataki na gwamnatin Ajeriya, ciki har da Ramdane-Youssef Tazibt, mamba a kwamitin koli na jam’Iyyar da kuma  Seddik Chihab, kakakin jam’iyyar RND. Sai dai tsohon ministan harkokin Wajen kasar Aljeriya Ali Benflis ya nesanta kansa da duk yunkuri na kasashen waje don daidaita al’amuran cikin gida.

Algerien Algeir - Proteste gegen Abdelaziz Bouteflika
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kramdi

Amirka ta yi kira ga bangarori dabam- daban da sua mutunta bukatun 'yan Aljeriya. Yayin da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka ta ce tana bin diddigin abin da ke faruwa a Aljeriya, amma kuma ba ta da niyyar yin shisshigi a lamrun siyasar kasar. Sai dai bayan da ya gana da takwaran aikinsa na Rasha Sergei Lavrov, ministan harkokin wajen Ajeriya Ramtane Lamamra ya ce kasarsa na bukatar kasashen waje taimaka wa Aljeriya rubuta sabon babin siyasa.

'Yan Aljeriya da ke da zama a Faransa sun ci gaba da nuna adawa da tazarcen Abdelaziz Bouteflika, suna masu cewa babu wata doka ta kundin tsarin mulki da ke bai wa shugaban kasa damar ci gaba da jan ragamar mulki bayan cikan wa'adinsa. Makonni da dama dubban 'yan Ajeriya suka shafe suna fitowa kan tituna don nuna adawa da mukin sai Mahdi ka ture da Boutefika da 'yan kanzaginsa ke gudanarwa. Sai dai har yanzu yana ci gaba da yin kunnen uwar shegu da kiraye-kirayen da 'yan Ajaeriya ke yi masa.