1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin siyasar Saliyo na kara dagulewa

Ahmed SalisuMarch 23, 2015

Rikicin siyasar Saliyo wanda ya yi sanadin sallamar mataimakin shugaban kasar Samuel Sam-Sumana daga bakin aiki na karuwa inda 'yan adawa ke shirin yanke kauna da gwamnati.

https://p.dw.com/p/1EvO7
Ernest Bai Koroma Wahlen in Sierra Leone
Hoto: AFP/Getty Images

Jam'iyyun adawa a Saliyo sun ce sun fara tunanin kauracewa yin aiki da gwamnatin kasar saboda abinda suka kira rashin bin ka'ida kan sallamar mataimakin shugaban kasar Samuel Sam-Sumana daga bakin aiki da aka yi.

'Yan adawar har wa yau sun ce za su shige gaba wajen ganin an kaddamar da shirin tsige shugaban kasar Ernest Bai Koroma daga gadon mulki kana sun ce za su nemi kotun kolin kasar da ta duba batun sallamar da aka yi wa Mr. Sam-Sumana daga aiki a makon jiya.

A kwanakin da suka gabata ne dai jam'iyyar da ke mulkin kasar ta kori mataimakin shugaban kasar bisa zargin yi mata zagon kasa, kana shugaban kasar ya sanar da sallamarsa daga bakin aiki. Al'ummar kasar da kungiyoyi masu rajin kare dimokradiyya dai sun soki lamirin shugaban kasar kan wannan batu.