1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin Ukraine na ta'azzara

April 21, 2014

Yarjejeniyar kawo karshen rikicin gabashin kasar Ukraine tana tangal-tangal

https://p.dw.com/p/1Blco
Hoto: DW/R. Goncharenko

Kasashen Rasha da Ukraine sun yi musanyen bakaken kalamai kan harbin da aka yi a yankin gabashin kasar ta Ukraine, inda aka hallaka uku daga cikin 'yan aware masu goyon bayan Rasha, yayin da wasu uku suka samu raunika. Harbin na jiya Lahadi ya faru a wajen binciken ababen hawa.

Mahukuntan birnin Moscow sun daura alhakin abun da ya faru kan masu tsattsauran ra'ayi na Ukraine, amma mahukuntan birnin Kiev suka ce wannan aiki ne na wasu daga kasashen ketere. Wannan harbi ya zama lamari na farko da ya jefa yarjejeniyar birnin Geneva cikin gadari, wadda aka sanya wa hannu ranar Alhamis.

Yarjejeniyar tsakanin kungiyar Tarayyar Turai, da Rasha, da Ukraine da kuma Amirka ta tanadi daukan matakai domin dakile ruruwar rikicin cikin yankin gabashin Ukraine. Gobe Talata mataimakin Shugaban Amirka Joe Biden zai gana da Shugaban wucin gadi na kasar ta Ukraine Oleksander Turchinov da Firaminista Arseny Yatseniuk, yayin ziyara ta kwanaki biyu da zai kai.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu