1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin ´yan takife a yankin Niger Delta a Nijeriya

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB8

´Yan takife a Nijeriya wadanda suka yi garkuwa da wasu baki 4 ma´aikatan mai makonni biyu da suka wuce, sun ce a shirye suke su ci-gaba da rike mutanen har wasu shekaru masu zuwa. A hirar da aka yi da su ta wayar tarho a ranar alhamis, mutanen 4 wadanda suka hada da Ba-amirke daya da dan Birtaniya da dan kasar Honduras da kuma dayan dan Bulgariya, sun ce ba sa cikin koshin lafiya. Kamfanin dillancin labarun Reuters ya labarto cewar ´yan takifen sun yi barazanar harba makamai masu linzami akan wuraren hakan mai na Nijeriya. ´Yan takifen suka ce daga gobe litinin zasu fara kai hare hare akan motocin daukar mai a yankin Nijer Delta face gwamnati ta sako shugabannin su biyu da aka daure kuma ta mika musu ikon tafiyar da harkar mai a cikin kasar.