1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin palasdinawa

May 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuM7

Dakarun kasar Izraela sun kashe yan palasdinawa guda uku, a wata muswayar wuta mai karfi daya gudana tsakanin bangarorin biyu a wani kuyen dake arewacin gabar kogin Jordan.

Wadanda suka rigamu gidan gaskiyan dake zama yan kungiyar Jihad Islamia,sun gamu da ajalinsu ne a garin Silat al-Harithiya dake yammacin Jenin.

Kakakin rundunar sojin Izraelan dai ya bayyana cewa ,palasdinawan sun fara bude wuta ne wa yansandan dake kann iyakokin dake gudanar da aikin kame a wannan gari,daga nan ne jamian tsaron suka mayar da martani,tare da kashe uku daga cikinsu.Wannan kisan da akayi yau dai ,ya kawo ga adadin mutane 5,678 kenan suka rasa rayukansu da barkewan sabon rikici na biyu a yankin palasdinawan a watan septamban 2000,mafi yawansu kuwa larabawan palasdinu.