Rikon sakainar kashi ga makarantun firamaren Najeriya

Shirin na Abu na Mu ya yi nazari ne kan yanayin tabarbareawar ilimi a Najeriya musamman a makarantun firamare da ke zaman tushen kowane ilimi.

Wannan matasala dai ta jima ana kokawa da ita, ta yadda ma al'umma ke wa harkar ta ilimi a Najeriya kallon iya kudinka iya shagalinka, wato ma'ana iya karfin tattalin arzikinka iya yanayin karatun da yaranka za su samu kasancewar akwai makarantun kudi. Shin ina matsalar take kuma ta wacce hanya ko hanyoyi za a iya shawo kan matsalar, ganin cewa matsalolin ana fuskantarsu ne a makarantu mallakar gwamnati da 'ya'yan talakawa ke halarta? Shin matsalar daga iyaye ne ko malamai ko kuma gwamnati ko kuwa ta kowa da kowa ce? Wannan batu ne dai shirin ya yi nazari a kai domin kuwa masu iya magana na cewa ilimi shi ne gishirin rayuwa wanda idan babu shi to tabbas za a iya fuskantar wasu matsaloli kana ilimin firamare shi ne tushe ko kuma tubali na ko wanne ilimi.

Now live
mintuna 09:43
Duka rahotanni | 03.12.2018

Rikon sakainar kashi ga makarantun firamaren Najeriya

Sanunsi Surajo tsohon sakataren ilimi ne na karamar hukumar Kaduna ta Kudu a jihar Kadunan Najeriya, ya kuma yi karin haske kan yadda makarantun firamaren mallakar gwamnati suka lalace. Haka shi ma Jafaru Ibrahim Sani shi ne kwamishinan ilimi na jihar Kaduna a Tarayya Najeriya ya yi nasa tsokacin bayan tambayarsa , shin wadanne irin matakai suke dauka domin dakile wadannan matsaloli da iyaye da ma al'umma ke bayyanawa dangane da tabarbarewar ilimi da ake ganin yana da alaka da rashin inganta al'amuran koyo da koyarwa a makarantun firamare musamman mallakar gwamnati?

Daga cikin iyayen ma da muka zanta da su, akwai wata uwa da ke da lalura ta rashin gani, ta kuma bayyana irin kalubalen da su da yaransu da ke da irin wadannan lalurori na ji ko gani ke fuskanta a makarantu. A latsa shirin mai dauke da sauti don jin cikakken bayani.

Bayanai masu kama

Rahotanni masu dangantaka