1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani a batun tsaron Najeriya

April 22, 2014

Batun rashin zaman lafiya da ake fama da shi a Arewacin Tarayyar Najeriya, lamarin yana neman rikidewa izuwa siyasa tsakanin gwamnati da masu adawa da ita.

https://p.dw.com/p/1BmDQ
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu

Wasikar da gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako, ya aikawa gwamnonin jihohin arewacin kasar inda yake zargin gwamnatin Najeriya na da hannu a kan batun rashin tsaro, wasikar na ci gaba da haifar da cece-kuce duk kuwa da martani da gwamnatin ta mayar.

To wasikar ta gwammana Murtala Nyako da ke neman zama allurar da za ta iya tono garma, saboda nauyin batutuwan da ya tabo dukkaninsu da suka shafi rashin tsaron da ake fama dashi, kama daga hare-haren da ya ce ana fakewa da Fulani ke yinsu, ya zuwa neman a janye sojojin daga jihohin Adamawa da Borno da Yobe. Tare da jefa tambaya yana kalubalantar gwamnatin Najeriyar ta fito karara ta bayyana wadanda ke kashe-kashen da suka jefa kasar cikin mamaki, zargi da ma yanayi na dimaucewa.

Fitowa karara a fili da gwamman ya yi da ake wa kalon mutum mai matsayi ya bugi girji ya yi abin da ke kama da tonon silili, saboda ganin matsayinsa na gwamnan da ya kamata na da masaniya a kan bayanai na tsaro da ba ko wane dan kasa ke da ikon samunsu ba, ya sanya maida murtani inda kungiyar dattawan arewacin Najeriyar ta ce dole ne a bincika, saboda nauyin batun. Barrsiter Solomon Dalung jigo ne a kungiyar.

‘'Tun daga Maiduguri har zuwa Benue da Nassarawa, kai har ma jihar Katsina. A hankali a hankali yanzu yankin arewa ta shiga cikin tsaka mai wuya na rigingimu ko na kungiyar Ahlu Sunnah Li Da'awatti Waljihad da aka fi sani da Boko Haram, ko kuwa na wasu irin sababbin Fulani masu yawo da jirgi mai saukan ungulu, maimakon shanu da aka san su da su, suna dauke da manya-manyan makamai. Wadannan abubuwa da suka tara da ma ganin an kafa dokar ta-baci a jihohi uku, amma duk da haka ‘yan kungiyar tsageru suna kai hare-hare suna cin karensu ba babbaka. To wanene kenan ya tsira?''

Alamun harzukar da gwamnatin ta yi a kan wasikara ta Nyako da ke zama mai doyin baragurbin kwai ga gwamnatin ta Najeriya inda ta maida martani tana mai cewa, cin amana ne domin kuwa gwamna Nyakon ya ci moriyar ganga ne a yanzu ya yasheta. Amma ga Dakta Sadeeq Abba, masanin kimiyyar siyasa da ke jami'ar Abujan Najeriya ya ce akwai bukatar nazari da ma la'akari da bayanan da ke cikin wasikar.

‘'Duk maganganun da gwamna Murtala Nyako ya fitar a wasikarsa, ba wani sabon abu ba ne. Domin kowa yasan da gaskiya amma ba wanda ke son ya fadeta, amma kar a manta fa Nyakon nan tsohon soja ne, kuma wanda ya rike mukamai da yawa a fannin tsaro a Najeriya, don haka bana tsamanin zai fita ya yi maganar kasuwa ba kawai wanda baya da wasu hujjoji. Abin yi shine in dai gwamnatin Najeriya ba ta gamsu da maganganun da ya yi ba, to sai a kawo shi a gaban hukuma ya gabatar da shaidunsa a kan wannan bayanai da ya fitar''.

A yayin da masharhanta ke nuna hatsarin da ke tattare da cece-kuce a tsakanin fadar gwamnatin Najeriyar da gwamnan na jihar Adamawa, ga Alhaji Garba Umar jigo a jam'iyyar PDP, na mai bayyana cewa wannan na iya zama hanyar da za ta iya rarrabe aya da tsakuwa, a kan matsalar tsaro da aka dade ana zargin wanda ke da laifi.

‘'Ai gara ma su yi fito na fiton, daga nan sai gaskiya ta fito domin in suka yi shiru mun san abin da suke ciki ne? su suke da jami'an tsaro da hanyar samun bayanai da wadanda za su ba su labarai. Gwamna na da tsarinsa na samun bayanai, domin haka a tsakaninsu ne za a samu maslaha, a tsakaninsu gaskiyar za ta fito''.

Duk da kokarin fito da gaskiyar lamarin, ga talakan Najeriya abin da yake fata shi ne samun wanzuwar zaman lafiya, domin kuwa mutanen biyu a baya tare ake ganinsu suna shan shayi.

Mawallafi: Uwais Abubakar Idris
Edita: Usman Shehu Usman