1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rudani ya sake barkewa a Jam'iyyar PDP

Ubale Musa | Yusuf Bala Nayaya
December 1, 2017

Mako daya kafin babban zabe na kasa na jam’iyyar PDP ta adawa a Najeriya wani sabon rikicin cikin gida na barazanar raba kan jam'iyyar da ke da fatan gina sabo na ginshikin tunkarar zabe a cikin karfi.

https://p.dw.com/p/2ocbD
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Cikin fata da buri ne dai kotun kolin tarrayar najeriya ta dauki jam'iyyar PDP ta adawa ta mika a hannun Ahmwed Mohammed makarfi domin jagoranta. To sai dai kuma wani rikicin cikin gida na neman komawa zuwa gidan jiya tare da jam'iyyar na fuskantar barazanar taruka guda Biyu a karshen makon da ke tafe.

PDP dai na fatan babban taron jam'iyyar zai kai ga ginan sabon gishikin da ke iya kaiwa ga bata damar sake gwarawa da kila cin zabe nan da shekaru biyun da ke tafe.

Karikatur Nigeria PDP Krise
Akwai kwantaccen rikicin shugabanci a PDPHoto: DW

To sai dai kuma kokari na fitar da shugabannin da za su ja ragamar jam'iyyar ya zuwa babban zaben na neman gaggarar 'yan cikin gidan na Wadata da har yanzu kansu ke dawa sannan kuma ke  kara dagun murya a cikin bainar jama'a.

Duk da cewar dai a baya hakarkari ya kwanta, sakamakon tabbatar da mukamin shugabancin jam'iyyar ya zuwa sashen Kudu maso Yammacin Najeriyar,  jefar da wannan tsarin tare da bude takarar ya zuwa daukacin manyan sassan kudancin kasar guda uku dai na zaman ummul'aba'isin sabon rikicin da ke barazanar kaiwa ga sake rabewar PDP gida biyu.

Ko bayan turjiya ta 'ya'yan jam'iyyar daga sashen na Kudu maso Yamma ga abun da suke kallon fashi da tsakar rana ya zuwa sashen Kudu maso Kudanci na kasar, can ma a sashen arewacin kasar dai ana gurnani bayan da jam'iyyar ta tsuke mukamai na takara zuwa ga jihohi akasin abun dake akwai a sashen na Kudu.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Gidan Wadata Plaza Abuja hedikwatar PDPHoto: DW/U.Haussa

Alal Misali dai duk da 'yan takara da daman gaske da ke da bukatar mataimakin shugaban jam'iyyar daga sashen Arewa maso Gabas, yanke shawarar tura mukamin zuwa jihohin Bauchi da Gombe dai ya har zuwa wasu a ciki na masu takarar irin su Inna Chiroma daga Yobe da ke fadin ko mutuwa ko yin rai. Haka can ma a Kano dai Hajiya Baraka Sani na fadin an saba bayan mika mukamin shugabar matan jam'iyyar zuwa ga Jihohin Kebbi da Sokoto maimakon kyaleshi ga daukacin 'yan jam'iyyar da ke yankin na Arewa maso Yamma.

Abun jira a gani dai na zaman dabarun 'yan lemar a kokari na tabbatar da tushe mai kwari da yake iya kai karshen mulkin masu tsintsiya na shekaru Hudu.