1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rundunar Amirka ta wanke sunan sojin kasar daga zargin kisa a Ishaqi

June 3, 2006
https://p.dw.com/p/Buva
Sanannen dan wasan Faransa, Zinedine Zidane
Sanannen dan wasan Faransa, Zinedine ZidaneHoto: AP
Rundunar sojin Amirka ta ce wani bincike da ta gudanar akan zargin yiwa fararen hula kisan gilla cikin watan maris a garin Ishaqi dake Iraqi, ya wanke sojojin ta daga wannan zargi. Da farko jami´an Iraqi sun ce sojoji Amirka sun harbe mutane 11 dukkan ´yan gida guda a wani samame da suka kai cikin wani gida, wanda daga bisani aka kai masa harin makami mai linzami. Binciken da Amirka ta yi ya gano cewar mutum 4 kadai aka kashe. Mataimakin hafsan dakarun kasa da kasa a Iraqi, manjo Janar William Caldwell ya fadawa wani taron manema labarai a birnin Bagadaza cewa sojojin Amirka ba su aikata wani laifi ba, a saboda haka ba za´a sake gudanar da sabon bincike ba.