1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ruruwar wutar rikici a gabashin Ukraine

November 10, 2014

Ministan harkokin wajen Jamus, ya nuna damuwarsa a wannan Litinin, kan yadda lamura ke ci gaba da yin kamari a yankunan gabashin Ukraine.

https://p.dw.com/p/1Dk8R
Frank-Walter Steinmeier Kasachstan Jerlan Idrissow
Hoto: picture-alliance/dpa/Hendrik Schmidt

Frank-Walter Steinmeier y ayi kira ga bengarorin da suka hada, da na gwamnatin Ukraine da 'yan awaren gabashin kasar, da ma kasar Rasha, da su mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma ta ran biyar ga watan Satumba a birnin Minsk na Belarus.

Shugaban Diflomasiyar kasar ta Jamus ya yi wadannan kalamai ne yayin wata ziyara da ya kai a Kazakhstan, inda ya ce jarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma, na ci gaba da fuskantar kalubane tun farkon ta. Daga na su bengare wakilan kungiyar tsaro da halin kan Turai ta OSCE, masu saka ido kan batun tsagaita wuta a gabashin kasar ta Ukraine, sun nuna damuwarsu kan yadda su ke ganin tankokin yaki masu yawan gaske a yankunan dake hannun 'yan awaren.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Suleiman Babayo