1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rwanda ta soke hukuncin kissa a dokokin ta

July 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuFO

Komishinar hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kulla da kare haƙƙoƙin Bani Adama, Louis Arbour,ta yabawa gwamnatin ƙasar Rwanda, a game da matakin da ta ɗauka na soke hukuncin kissa daga dokokin ƙasa.

Jiya Rwanda ta bayyana wannan mataki, wanda ta ɗauka da zumar,gudanar da shari´a, ga dukkan mutanen da ake zargi da hannu a cikin ta´adin da ya wakana a wannan ƙasa a shekara ta 1994.

A game da haka ,hukumomin Kigali, sun yi kira ga ƙasashen dunia, wanda su ka baiwa yan Rwandar da ake tuhuma da wannan lefi mafakar siyasa, su taso ƙeyar su zuwa gida.

A cewar Louise Arbour, wannan mataki da Rwanda ta ɗauka zai taimaka matuƙa, wajen binciko gaskiyar al´ammuran da su ka wakana a lokacin kissan ƙare dangi, da ya rutsa da al´ummar ƙasar Rwanda.