1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saɓani kan sabon tsarin mulki na Masar

December 1, 2013

Akwai sauran aiki kan rubuta sabon kundin tsarin mulkin ƙasar wanda ake ta yin tankiya akai

https://p.dw.com/p/1ARLb
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar rubuta kundin tsarin mulkin ƙasar Masar, ta yi watsi da ƙudirin da ya nemi gudanar da zaɓen 'yan majalisa kafin na shugaba ƙasa, abin da ya ƙara haifar da rashin tabbas a ɓangaren siyasa ƙasar, kan jadawalin mayar da ƙasar bisa tafarkin demokraɗiyya.

'Yan majalisar 33 daga cikin 50 da Shugaba gwamnatin wucin gadi Adly Mansour ya naɗa, sun kaɗa ƙuri'ar ƙin amince wa da wannan ƙudiri, yanzu tilas sai an sake fasalin kundin tsarin mulkin. Wasu daga cikin mambobin majalisar rubuta kundin tsarin mulkin sun nemi gudanar da zaɓen shugaba ƙasa da farko kafin na 'yan majalisa, saboda rashin ƙarfin jam'iyyun mara sa alaƙa da addini. Amma mafi yawan mambobin majalisar rubuta kundin tsarin mulkin ƙasar, sun amince da kotun soja ta hukunta fararen hula bisa wasu laifuka na musamman. Ƙasar ta Masar tana cikin ruɗani siyasa tun ranar 3 ga watan Yuli da sojoji suka kifar da zaɓaɓɓiyar gwamnatin Mohammed Mursi. A wannan Lahadi 'yan sanda sun yi amfani da hayaƙi mai saka hawaye kan masu nuna goyon baya ga tsohuwar gwamnatin.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane