1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sa In Sar Falasdinu da Isra'ila

July 25, 2017

Shugabannin falasdinawa a birnin kudus, sun ce ba za su janye matakinsu na kauracewa masallacin Al Aqsa ba, sai har Isra'ila ta janye dukkanin matakan tsaron da ta kafa a masallacin.

https://p.dw.com/p/2h7KA
Palästina - Israel - Konflikt - Mahmoud Abbas
Hoto: Getty Images/AFP/A. Momani

Batun tsaurara tsaro da na'urori a masallacin da musulmi ke darajawa a makon jiya dai, ya haddasa fito-na fito tsakanin musulmi da kuma Isra'ilawa. Su dai falasdinawan sun kekashe kasa ne, suna mai cewa sun kure hakurinsu bayan kwace masu yankuna, yanzu kuma Isra'ilar ta hau kan masallacin na Al Aqsa da suke karramawa.

Wannan dai waje ne da ke da muhimmanci ga musulmi da yahudawa gami da mabiya addinin kirista. A wannan Litinin, gwamnatin Isra'ila ta soma janye na'urorin binciken da ta kakkafa a kofofin shiga masallacin. Kuma bayan matsin lamba daga bangarori daban-daban na duniya, jami'an tsaron Isra'ilar sun fada a yau Talata cewar za su amince da shawarwarin cire matakan tsaron da suka sanyawa wajen.