1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saakashvili ya doshi hanyar lashe zaɓen shugaban Georgia a zagayen farko

January 6, 2008
https://p.dw.com/p/CkxL

Bisa ga dukkan alamu shugaban Georgia Mikhail Saakashvili ya sake komawa kan mulki bayan zaɓen da aka gudanar a jiya asabar. Sakamakon jin ra´ayin masu zaɓe da aka gudanar bayan kuri´ar ta jiya ya yi nuni da cewa Saakashvili ya samu sama da kashi 50 cikin 100 na yawan kuri´un da aka kaɗa a zagaye na farko na wannan zabe. Shugaban ya fadawa magoya bayansa a hedkwatar jam´iyarsa dake birnin Tiblisi cewa zaɓen nasara ce ga Georgia. To amma ´yan adawa sun yi ƙorafi suna masu cewa an aikata ba daidai ba a zaben. Sun yi kira da a gudanar da wata zanga-zanga a yau lahadi don yin watsi da zaɓen. A wani lokaci yau kungiyar tsaro da hadin kai a Turai wadda ta tura massu sa ido a zabe kimanin dubu daya, zata tofa albarkacin bakinta dangane da zaɓen, amma wani wakilinta daga Jamus Dieter Boden ya nunar da cewa an tabka wasu kurakurai a zaɓen.