1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani kan dokar aure a Najeriya

Usman ShehuJuly 24, 2013

A wani mataki mai kama da ta yi amanta ta lashe, majalisar dattijan Najeriya ta ce ita kam bata halasat auren kananan yara ba.

https://p.dw.com/p/19Dda
to share – to copy, distribute and transmit the work to remix – to adapt the work Under the following conditions: attribution – You must attribute the work in the manner specified by the author or licensor (but not in any way that suggests that they endorse you or your use of the work). share alike – If you alter, transform, or build upon this work, you may distribute the resulting work only under the same or similar license to this one.
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

A wani abun dake zaman kama hanyar sauyin matsayi, majalisar dattawan Najeriya ta nisanta kanta daga kokarin halasta aure ga kananan yara mata a cikin Kasar. Duk da cewar dai an kira batu na shekarun sauya kasa, tuni dai maganar balagar mata a cikin tarrayar ta koma wani babban batun da ya kai ga jerin zanga- zanga a ciki da wajen majalisar dattawan kasar da a makon jiya ta haramta dokar da ta nemi kai'yade balagar matan kasar zuwa shekaru 18.

Afrika Kinder lachen
Kananan 'yan mata a Najeriya.....Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisar dai taga dumi tun daga farkon fari a lokacin da 'ya'yanta suka kai ga rabon gari a tsakanin masu tunanin addini tsantsa da kuma masu ganin zamani ya sauya kuma dole ne sauyin ya zama wajibi ga kowa a kasar. To sai dai kuma nasarar masu takama da addinin ta kuma bude sabuwar mahawarar da ta kai ga kusan fito na fito a tsakanin kunigyoyi na fararen hular kasar dake kiran ba'a isa ba da kuma 'yan majalisar dake fadin bakin alkalami ya riga ya gama bushewa.

Sanata Ahmed Sani Yarima dai na zaman dan majalisar dattawan kasar ta Najeirya daga jihar Zamfara, mutumin kuma da ya jagoranci adawa da kokarin gyaran kundin tsarin mulkin kasar, kuma a fadarsa kokarin gyaran sashen na zaman wani shirin kutungwilar da ta sha kaye da taimakon ubangiji.

Frauenpower in Nigeria
.....matan aure a NajeriyaHoto: AP

Sai dai kuma daga dukkan alamu tsallen murnar su Yariman na da sauran aiki, musamman ga daukacin 'yan bokon kasar ta Najeirya dake cewar ba zata sabu ba wai bindiga a cikin ruwa. An dai tsara ministar matan kasar ta Najeirya zata jagoranci kungiyoyin mata zuwa ga zauren majalisar  kasar domin nuna rashin gamsuwarsu da matakin dattawan. Ene Ede babbar jami'a ce a kungiyar Equity Advocates dake fafutukar tabbatar da 'yancin mata a kasar, ta kuma yi damarar shiga cikin tawagar matan da nufin sai baba ta gani kan matsayin nasu.

Abun jira a gani dai na zaman mafitar rikicin dake zaman zakaran gwajin dafi a tsakanin masu neman sauyin tsarin da kasar ke tafiya a kai ya zuwa irin na turawan yamma da kuma masu cewar babu gudu babu ja da baya cikin tsarin gado.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar/ UA