1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabani tsakanin masu adawa da shugaban Chadi

Dariustone Blaise/Mouhamadou Awal BalarabeApril 8, 2016

An samu baraka tsakanin shugabanin kungiyoyin fararen hula da ke neman ganin bayan mulkin Shugaba Idris Deby Itno na Chadi.

https://p.dw.com/p/1IS6i
Sudan Khartum Idriss Deby Präsident Tschad
Hoto: picture-alliance/dpa/E. Hamid/Ausschnitt

Tuni wasu daga cikinsu suka nesanta kansu daga ganawar da bangaren gwamnatin ya yi da mambobin hadakar da ke kyamar nau'in mukin sai madi ka ture a Chadi.

Babban abin da ke ci wa kungiyoyin na Chadi tuwo a kwarya dai, shi ne rawar da wasu mambobin gamayyar da ke adawa da manufofin gwamnati Shugaba Deby suka yi. Alal hakika dai shugaban kungiyar farar hula ta "Ca suffit" wato Baldal Oyamta da na kungiyar "Trop c'est trop" wato Barka Michel sun gana da manyan jami'an fadar shugaban kasa ba tare da izinin sauran takwarorinsu ba. Lamarin da ya tayar da hankulan sauran shugabanin kungiyoyin fararen hula saboda suna danganta wannan mataki da ba da kai domin bori ya hau.

Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar
Hoto: Getty Images/AFP/G. Cogne

Dadin dadawa kuma, Sakatare janar na gamayyar kungiyoyin kodagon Chadi ya yi gaban kansa wajen fitar da wata sanarwa da ke nuna cewar bangaren fararen hula za su shiga a dama da su a harkar zaben. Alhali cikin 'yan kwanakin da suka gabata sun janye mambobinsu daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar Chadi bisa zargin shirya zaben jeka na yika.

Gounou Vaima Ganfare da ke zama kakakin kungiyar "Ca suffit" ya ce har yanzu suna kan bakarsu ta juya wa Shugaba Idris Deby Itno baya, saboda haka ba da yawunsu aka dauki wadannan matakan ba.

Sai dai a bangaren jam'iyyun adawa da suka tsayar da 'yan takara a zaben na 10 ga watan Afirilu, suna ci gaba da daukan matakan da suka wajaba domin ganin cewar mulki ya salube daga hannu Deby a zagaye na biyu. Hasali ma sun saka hannu kan wata yarjejniya da ta tanadi kasa kuri'u da tsare su tare da kuma da rakasu. Sannan sun amince da mara wa duk dan takara na adawa da zai fafata da shugaban kasar Chadi na yanzu a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa.

Nasra Djimasngar wanda yake shugabantar jam'iyyar "Un Jour Nouveau" shi ya yi ruwa da tsaki saboda ganin cewar 'yan adawa sun zama tsintsiya madaurinki daya, lamarin da yake tsammani zai sa su magance magudin zabe.

Tschad N'djamena Zuschauer bei Pferderennen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Tuni dai Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya tura da manzo zuwa kasar Chadi domin ya dinke rikicin da ya kunno kai a fagen siyasa. Abdoulaye Bathily ya jagoranci ganawar farko da ta watse baram-baram, amma kuma zai sake zama da 'yan adawa da shugabannin kungiyoyin fararen hula a yammacin wannan Jumma'a. Sai dai kakakin kungiyar "Trop c'est trop" ya rigaya ya ce ba zai halarta ba, matukar dai ba a sako duk wadanda gwamnati ta kama kuma ta kai gidan yarin Amssinené tun makonni biyun da suka gabata ba.