1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabanin ra'ayi kan yaki da Boko Haram

June 21, 2013

Najeriya tana ci-gaba da daukar matakan dakile kungiyar Boko Haram tun bayan kafa dokar ta-baci a jihohi uku na yankin arewa maso gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/18uDk
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Hare-haren da kungiyar da ake kira Boko-Haram ta kaddamar sun shafi aikin makarantu musamman a Jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya. Kuma yanzu haka gwamnati ta tura kimanin dakaru 2000 cikin yankin tun bayan kafa dokar ta baci, domin kawar da kungiyar mai gudanar da aiyukan ta'addanci.

Tun lokacin da aka aiyana dokar ta-baci domin tunkarar kungiyar ta Boko Haram gwamnatin ke bayyana nasarar da take samu. Amma a baya-baya nan an samu cikas, musamman sakamakon hare-hare kan 'yan makaranta da aka fuskanta, kuma ana samun ra'ayi mabanbanta bisa matakan na soja. A tsakiyar watan Mayu cikin yankin arewa maso gabashin kasar aka kakaba dokar ta-baci a jihohi uku na Adamawa, da Borno da kuma Yobe. Amma yanzu fadan ya dauki sabon salo, inda 'yan kungiyar ke kai hari kan dalibai. Paddy Kemdi Njoku na daga cikin wakilan kungiyoyi masu zaman kansu:

''Abubuwan da suka janyo kungiyoyin kamar Boko Haram ga misali, ya dace a duba, kuma abin da muke yi ke nan a kungiyoyi masu zaman kansu. Ilmantar da mutane bisa nauyin da ke kansu. Horas da mutane zama 'yan kasa na gari. Magana da gwamnati domin tabbatar da samar da aiki, mutane su samu aiki, iyaye su bayar da tarbiyar da ta dace.''

Unruhe und Gewalt in Nigeria ARCHIVBILD
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Wani abu shi ne, yadda 'yan kungiyar ta Boko Haram ke maganar cewa suna neman kafa shari'ar Musulunci a cikin kasar. Shugaban Kiristoci na Kotolika da ke Abuja fadar gwamnatin ta Tarayyar Najeriya, John Onaiyekan ya ce, akwai wata munufa ta Boko Haram, inda suke amfani da wasu matsaloli wajen zama masu zazzafar ra'ayi, kuma ya yi nuni da wannan tsattsauran ra'ayi na 'yan kungiyar:

''Wadannan yara ina suka samo wannan ra'ayi na yadda suke bukatar yadda abubuwa za su kasance. Kuma suka dage dole sai sun mayar da kasar karkashin tafarkin Islama. Wannan shi ne tunanin Musulmai masu matsananci ra'ayi ko'ina duniya. Idan cin hanci ya yadu sai su ce domin rashin tsarin Islama ne, wanda shi ne addinin zaman lafiya. Babu zaman lafiya a duniya sai duk mun zaman Musulmai.''

Najeriya kasa ce mai mutane fiye da milyan 160, kuma mabiya addinin Kirista sun kai rabin al'ummar kasar. Yayin da gwamnatin kasar ta kafa dokar ta-baci sannan ta tura sojoji, domin tabbatar da zaman lafiya yankunan da ake samun tashin hankali, a daya hannu an kafa kwamitin ahuwa ga wadanda suka mika wuya. Emmanuel Nnadozie Onwubiko na wata kungiya mai zaman kanta, da ke rubuce-rubuce bisa kare hakkin dan Adam:''

Nigeria Notstand Islamisten Präsident Goodluck Jonathan Fernsehansprache
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

''Wannan babban sabani ne, saboda yaya a hannu daya za ka aiyana yaki da 'yan ta'adda, kuma a daya hannu ka nemi sasantawa, haka rashin dabara ce bisa yakan aiyukan ta'addanci.''

Tun farkon kafa dokar ta ta-baci gwamnati ta bayyana wargaza sasanonin 'yan ta'adda na kungiyar ta Boko Haram mai gwagwarmaya da makamai. Kuma sojoji na ci gaba da daukan matakan kawar da kungiyar cikin yankunan da ake artabu. Gwamnatin ta Najeriya karkashin Shugaba Goodluck Jonathan ta ce, za ta yi ahuwa ga 'ya'yan kungiyar wadanda suka yi watsi da makamai da dawowa daga rakiyar aiyukan ta'addanci.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar