Sabauwar zanga-zanga a Faransa

An cafke mutane 700 a Faransa, bayan wata arangama tsakanin dalibai masu zanga-zanga da jami'an 'yan sandan kasar.

Rahotanni sun nunar da caewa daliban na zanga-zangar nuna kin amincewarsu da tsaurara matakan shiga jami'a da kuma rage malamai. Wannan zanga-zangar dai na zuwa ne kwanani kalilan bayan fara wata zanga-zangar kin amincewa da karin kudin albarkatun man fetur a Faransan. Tuni dai Shugaba Emmanuel Macron na Faransan, ya sanar da cewa an dage batun karin, sai dai duk da haka masu fafutukar sun shirya gudanar da wata zanga-zangar a mako mai zuwa.

Rahotanni masu dangantaka