1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin dabarun shuka bishiyoyi a Kamaru

April 11, 2017

Sauyi ta hanyar maye gurbin bishiyoyin turaren da wasu nau-in na gida domin inganta muhalli da samar da katako da turakan wutar lantarki

https://p.dw.com/p/2b2rZ
Teaser Globalideas / ohne Logo – Kongo
Hoto: Jürgen Schneider

A yanzu dai mafi akasarin filaye a kasar Kamaru ana amfani da su ne wajan dasa bishiyar turare wadda ake amfani da ita wajen samar da katako ko kuma turakan wutar lantarki. Jama'a da dama dai a Kamarun sun mai da dasa wadannan Bishiyoyin Turaren a matsayin hanyar samun kudin shigar su. Amma kuma kasancewar bishiyoyin ya haifar da karancin ruwa da irin shuka a shekarun 1980, a wasu kauyukan kasar, sai dai kuma yanzu haka akwai wata kungiya a kasar da ke himmar kawo sauyi ta hanyar maye gurbin bishiyoyin turaren da wasu nau-in na gida.

Yadda wasu tarin tsuntsaye ke zama bisa bishiyoyin turaren kenan da kuma yadda suke saka gidan su wadda suke amfani da zaren ganyen bishiyar da ciyawa. Wadannan bishiyoyi dai sun kasance tamkar gida ne ga wadannan tsuntsaye, a kauyen Kingomen dake yankin arewa maso yammacin Kamaru.

Sai dai kuma wadannan bishiyoyi, ba yan gida bane kamar tsuntsayen, domin su an samo irin su ne daga Australia. An kawo irin ne a karnin da ya gabata wato karni na ashirin, kuma sun gurbata yanayin albarkatun kasar in ji wani daraktan wata kungiya mai zaman kanta wadda take gudanar da ayyuakan jin kai, Stephen Ndzerem wadda kuma shine ma jagoran masu aikin yanke bishiyoyin turaren da kuma maye gurbin su da wasu nau-i na gida.

Teaser Globalideas – Kongo
Hoto: Jürgen Schneider

Faduwar farashin kofi a shekarun 1970 dai na daga cikin dalilan da suka sanya jama'a dasa bishiyoyin turaren, kamar yadda Nzerem ya ce. Mutane da dama sun rasa aikin su sannan kuma ya zamo basu da wata hanya sai dai su dasa bishiyoyin domin samun ice da za su yi amfani da su.

Zuwa shekarun 1980, bishiyoyin sun kara yaduwa a wurare daban-daban wadda hakan kuma yayi sanadiyyar fadawa matsalar ruwa a kasar Kamaru baki daya da kuma bushewar iri, kusan ko ina ya zama a bushe.

Ciyar da iyalan ta da suka kai su takwas ya zama abu mai wuya ga Elizabeth. Yunwa kuwa ta zama damuwar kullum. Karancin ruwa da abinci da ya samo asali tun a shekarun 1980, shi ne ma abin da ya sanya Stephen shugaban kungiyar SHUMAS a takaice daukar matakin yanke bishiyoyin. Don haka ne ma a shekarar 2000, tare da taimakon wasu manoma, ya kaddamar da shirin maye gurbin bishiyoyin turaren wadda har ya ba su damar sare bishiyoyin kimanin miliyan 3.

Suna wannan aikin ne dai tare da tallafin wasu kungiyoyi biyu masu zaman kan su daga Birtaniya. Stephen dai ya bayyana wasu nau-in itatuwan da suka maye gurbin bishiyoyin turaren har kusan nau-i 60.