1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin hare-hare a kusa da Chibok

June 29, 2014

Wasu 'yan bindiga da ake dangantawa da 'yan Boko Haram sun kai hari a wasu majami'u da ke cikin garuruwa hudu da ke kusa da Chibok na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/1CSOo
Nigeria Soldaten Archiv 2013
Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Mazauna garuruwan sun nunar da cewar an kashe kiristoci da dama lokacin da suke tsaka da ibada da kuma lokacin da suka nemi ranta a na kare domin tsira da rayukansu.

Su dai 'yan bindigan sun yi amfani da babura wajen harba boma-boman a wuraren ibadan na garuruwan Ngurojina da Kautikari da Karakau da kuma Kwada, dukkaninsu a jihar Borno. sai dai har yanzu babu wata kafa da ta yi bayani kan yawan mutanen da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikata lokacin wadannan hare-hare. Su ma dai hukumomin tsaron tarayyar Najeriya har yanzu ba su ce komai ba game da wannan al'amari.

Borno dai na cikin jihohi uku na yankin arewa maso gabashin Najeriya da ke ci gaba da fuskantar hare-haren da ake dora alhakkinsu kan kungiyar Boko Haram duk kuwa da dokar ta-bacin da gwamnati ta kafa tun sama shekara guda da ta gabata. A wannan yanki ne ma 'Yan Boko Haram suka sace 'yan mata 'yan makaranta sama da 200 wadanda har yanzu ba a kubutar da su ba.

Mawallafi: Mouhamadou Auwal Balarabe
Edita : Zainab Mohammed Abubakar