1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin tuhume-tuhume kan Shugaba Zuma

Yusuf BalaMay 23, 2016

Cikin tuhume-tuhumen dai sun hadar da wanda ake zargin hannunsa a badakalar cinikin makamai a karshen shekarun 1990.

https://p.dw.com/p/1Isji
Südafrika Kapstadt Jacob Zuma Präsident
Shugaba ZumaHoto: Reuters/M. Hutchings

A safiyar Litinin din nan ce ake sa ran masu gabatar da kara a Afirka ta Kudu za su maida martani kan hukuncin cewar shugaba Jacob Zuma zai fiskanci tarin tuhume-tuhume 750 kan harkokin da suka shafi cin hanci da rashawa.

Cikin tuhume-tuhumen dai sun hadar da wanda ake zargin hannunsa a badakalar cinikin makamai a karshen shekarun 1990, wadanda aka janye su a shekarar 2009 abin da ya ba wa shugaban dama ta tsayawa takara, sai dai a watan da ya gabata babbar kotun kasar ta bayyana cewa an tafka kuskure a wancan hukunci kuma akwai bukatar a sake taso da shi dan sake nazari.

Wannan dai na kara tulin kalubale a gaban shugaba Zuma wanda dama ke fama da tuhuma bayan da babbar kotun kasar ta ce ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar kutse bayan da ya dauki miliyoyin kudade daga baitil malin al'umma dan kawata gidansa.