1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabiya ta yi shailar zama ´yantacciyar kasa guda daya

June 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuvI

Sabiya ta ayyana kanta a matsayin ´yantacciyar kasa daya bayan shawarar da Montenegro ta yanke ta ballewa daga abin da ya saura daga tsohuwar kasar Yugoslabiya. Dukkan wakilai 126 da suka halarci zaman majalisar dokoki mai kujeru 250 sun goyi da bayan matakin da gwamnati da kuma sauran ma´aikatun gwamnati suka dauka na kammala dukkan shirye shiryen da suka wajaba na raba tarayyar Sabiya a cikin kwanaki 45 masu zuwa. ´Yan adawa sun kauracewa zaman majalisar na musamman. Tun a ranar asabar Montenegro ta yi shailar samun ´yancin ta a hukumance. A wata kuri´ar raba gardama da aka gudanar kimanin makonni biyu da suka wuce masu zabe a Montenegro sun kada kuri´ar amincewa da raba gari da Sabiya.