1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon adadin 'yan gudun hijira daga hukumar HCR

Salissou BoukariAugust 28, 2015

A wani sabon adadi, hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin 'yan gudun hijira dubu 300 ne suka ketara tekun Bahar Rum da zimmar shiga Turai.

https://p.dw.com/p/1GNSH
Melissa Fleming
Melissa FlemingHoto: United Nations Geneva/Jean-Marc Ferré

Wannan adadi dai, adadi ne na daga farko wannan shekara kawo yanzu, yayin da a shekarar da ta gabata ta 2014 ga baki dayan adadin yake na mutun dubu 219. Rahoton ya kara da cewa a kalla mutane 2.500 ne suka hallaka a kokarinsu zuwa tashar ruwan kasar Italiya, amma kuma cikin wannan adadin babu na mutane 200 da suka rasu a ranar Alhamis a yankin ruwan Libiya.

Yayin da take magana ga manema labarai, kakakin hukumar 'yan gudun hijira ta HCR Melissa Fleming, ta ce yadda ake cinkushe mutane cikin jiragen ruwan ne ke sanadin mutuwarsu. Wasu daga cikin wadanda suka tsira da rayukansu a hadarin na ranar Alhamis dai, sun sanar da yadda ake tilasta musu zama cikin wani dan kankanan fili cikin jirgin ruwan, da kuma yadda masu shigar da su din ke karbar kudade.