1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon fata ga Firaministan Turkiya

March 31, 2014

Jam'iyyar AKP ta Firaminista Racep Tayyip Erdogan ta samu nasarar lashe zaben kananan hukumomi da sama da kaso 45 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada.

https://p.dw.com/p/1BZIV
Kommunalwahlen Türkei Erdogan 31.03.2014 in Ankara
Hoto: picture alliance/AP Photo

Samun nasarar lashe zaben kananan hukumomin da aka gudanar a Turkiyan da jam'iyyar AKP ta Firaminista Racep Tayyip Erdogan ta yi, ya nuna karara cewa akwai yiwuwar ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar da kuma samun galaba a zaben da ke tattare da kalubale da kuma rikita-rikita bisa zargin hannu a wata gagarumar badakala ta cin hanci da rashawa da ta tilasta wa wasu ministocinsa ajiye mukamansu.

Firaminista Erdogan dai bai taba boye fatansa na tsayawa takarar shugabancin kasar a zabuka masu zuwa da za a gudanar a watan Agustan wannan shekarar ba wanda in har ya samu nasara zai kasance shugaban kasar Turkiya na farko da aka zaba ta hanyar dimokardiyya, sai dai kuma yana fuskantar gagarumin kalubale daga babban abokin hamayyarsa wanda kuma yake da tasiri sosai a kasar ta Turkiya wato sanannen malamin addinin Islama da ke zaune a Amirka Fatehullah Gulen, baya ga badakalar cin hanci da almundahana da kudaden jama'a da ta kunno kai a gwamnatin nasa a 'yan kwanakinnan.

Kalubale daga ketare

Erdogan dai na zargin Gulen da yin amfani da wasu jami'an tsaro da ma alkalai da ke goyon bayansa wajen hada masa gadar zare da ma kulla masa makarkashiya a kokarin da suke na ganin bayan gwamnatinsa. Da yake bayani a ofishin jam'iyyarsu ta AKP a gaban dubban magoya bayansa bayan da aka bayyana sakamakon zaben, Erdogan cewa yayi.....

Kommunalwahlen Türkei
Hoto: Reuters

"Duk masu cika baki da yin kumfar baka a kan gwamnatinmu yau an nuna musu iyakarsu domin kuwa an rufe bakin tsanya, masu siyasar gaba yau sun fadi kasa warwas, masu siyasar kokarin ganin bayanmu sun sha kasa, masu yin siyasar batanci su ma sun sha kaye."

Tuni dai babbar jam'iyyar adawa ta CHP ta bayyana aniyarta ta kalubalantar zaben a gaban kuliya. Su ma dai sauran jam'iyyun adawar Turkiyan na da ja dangane da batun badakalar cin hanci da aka bankado a cikin gwamnatin ta Erdogan kamar yadda shugaban jam'iyyar adawa ta National Movement Devlet Bahceli ke cewa....

"Turkiya na neman kasancewa karkashin ikon mutum guda, har yanzu bai gama wanke kansa daga zargin cin hanci da ake wa gwamnatinsa ba. Yanzu ma abun da sakamakon zaben ya nuna ke nan. Gwamnatin tana cikin badakalar cin hanci da rashawa kuma har yanzu bai wanke kansa ba."

Kommunalwahlen Türkei
Hoto: AFP/Getty Images

Shirin yin ramuwar gayya

A jawabin da yayi ga dinbin magoya bayan nasa, Erdogan ya sha alwashin hukunta duk wasu da ya bayyana da masu kokarin aikata ta'addanci ga yanayin siyasar kasar da ya ce ya zama dole su girbe abun da suka shuka. A dangane da haka wasu na ganin Erdogan zai yi amfani da wannan dama wajen ci gaba da musguna wa 'yan adawa. Wani dan jarida a kasar Kadri Gürsel ya bayyana fargabarsa kan wannan batu na daukar fansa inda ya ce......

"In har bayan kammala wadannan zabuka gwamnati ta ce za ta dauki wani mataki na ramuwar gayya a kan 'yan adawa, to tabbas za a fuskanci babbar matsala a wannan kasar daga nan kuma sai a fuskanci gagarumin tashin hankali."

Jam'iyyar ta AKP dai ta samu nasarar lashe sama da kaso 45 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zabukan kananan hukumomin kasar wanda hakan ya bata rinjaye fiye da wanda ta samu a zabukan shekara ta 2009 inda ta samu kaso 39 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mohammad Nasiru Awal