1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon fata game da batun nukiliyar Iran

November 8, 2013

Kasashe biyar da ke da karfin fada a ji a duniya da kuma Jamus na bayyana kyakkyawan zato a tattaunawarsu da Iran.

https://p.dw.com/p/1AEP4
Hoto: Reuters

A dai dai lokacin da sabon zababben shugaban kasar Iran ke cika kwanaki 100 a kan karagar mulki, an fara wata sabuwar tattaunawa kan batun makamashin nukiliyar kasar tsakanin Iran din da kasashen yamma a birnin Geneva na kasar Switzerland.

Tun dai daga shekara ta 1979 da dangantaka tsakanin Amirka da Iran ta yi tsami, ba a sake samun wani kusanci na diflomasiyya tsakanin kasashen biyu ba sai a cikin watan Satumban da ya gabata, inda shugaban Amirka Barack Obama ya tattauna ta wayar tarho da sabon zababben shugaban Iran din Hassan Rouhani, yayin da a hannu guda kuma sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya gana da takwaransa na Iran din Mohammad Dschawad Sarif a zauren Majalisar Dinkin Duniya, kan batun makamashin nukiliyar Iran din da ake ta takaddama a kansa.

Wannan dai ana ganin wani sabon salo ne na neman sasantawa da kasashen na yamma da Rouhani ya bullo dashi, tun bayan da ka zabe shi a matsayin sabon shugaba duk kuwa da cewa a baya shugaban addini na kasar ta Iran Ayatollah Ali Khamenei, ya sanar da cewa abu ne mai matukar wahala a samu wata kyakkyawar alaka tsakanin Amirka da Iran.

epa03812039 A handout photo made available by Iran's supreme leader website shows Iran's Supreme Leader Ayatollah Ali Khamenei (L) gives the endorsement letter to the new President Hassan Rowhani (R), during a ceremony for his confirmation as Iran's President in Tehran, Iran, 03 August 2013. EPA/IRAN SUPREME LEADER WEBSITE / HANDOUT
Shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei da shugaban kasa Hassan Rouhani.Hoto: picture-alliance/dpa

Wani kwararre kan harkokin Iran din da ke cibiyar kimiyyar siyasa a birnin Berlin na nan Jamus Walter Posch, na da ra'ayin cewa wannan matakai da Rouhani ke dauka ba ya rasa nasaba da mashawartan da yake tafiya da su.

Ya ce " Rouhani na da kwararrun mashawarta wadanda za su iya kyautata alakar Iran da sauran kasashen duniya, wanda hakan ke nuni da cewa kila a wannan karon Iran din da gaske take tana son a kawo karshen takaddamar da ake yi a kan shirin makamashin nukiliyar na ta".

Ko da a watan Oktoban da ya gabata ma dai, an yi irin wannan tattaunawa da kasashe biyar da ke da karfin fada a ji a duniya da kuma Jamus, wanda bayan duba shawarwarin da suka yanke a yayin taron kasashen da suka hadar da Amirka da Rasha da China da Birtaniya da Faransa da kuma Jamus din, suka amince da sake zama a teburin shawarar da Iran.

Kakakin jami'ar hulda da kasashen ketare ta Kungiyar Tarayyar Turai Catherine Ashton da ke jan ragamar tattunawar Michael Mann, ya ce a shirye suke su saukaka takunkumin karya tattalin arzikin da suka kakabawa Iran din in har da gaske take za ta basu hadin kan da suke bukata.

Ya ce " In har bangaren Iran a shirye yake da ya kawo karshen abubuwan da ake tababa a kansu, to a shirye muke mu sassauta kamar yadda muka ce. Mun sanya abubuwan da muke bukata da su a kan faifai, kuma za su ci gaba da kasancewa a kan faifan, ina mai tabbatar da cewa yanzu wuka da nama na hannun Iran domin shawo kan manyan matsalolin da ke kawo cikas".

Iran Atomprogramm Atom Ahmadinedschad Fordo
Wani sashe na tashar makamashin nukiliyar Iran.Hoto: AP Photo/Iranian President's Office

Tuni dai ministocin harkokin kasashen waje na Birtaniya da Jamus da Faransa da kuma Amirka suka isa birnin na Geneva domin ci gaba da tattaunawa da Iran din da a wannan karon ake fatan za a samu kyakkyawan sakamako.

Takunkumin tattalin arzikin da kasashen yamma suka kakabawa Iran dai na taka muhimmiyar rawa wajen saka kasar cikin halin tsaka mai wuya, inda hauhawan farashi ya karu da kaso hudu, yayin da kuma rashin aikin yi ya karu da kimanin kaso 11, wanda hakan ya kawo cikas a kokarin da Rouhani ke yi na cika alkawuran da ya dauka a yayin yakin neman zabe.

Kasashen na yamma dai na fargabar cewa Iran na kokarin mallakar makaman kare dangi ne, zargin da a ko da yaushe Tehran din ke musantawa tana mai cewa shirinta na zaman lafiya ne.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani