1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon jadawalin zaɓuka a Nijeriya

November 24, 2010

A ranar 9 ga watan Afrilun 2011 ne al'ummar Nijeriya za ta jefa ƙuri'ar zaɓen shugaban ƙasar.

https://p.dw.com/p/QGe8
Shugaban Nijeriya, Goodluck JonathanHoto: picture-alliance/dpa

Hukumar zaɓen Nijeriya mai zaman kanta INEC ta ayyana tara ga watan Afrilun baɗi idan Allah ya kaimu a matsayin ranar gudanar da zaɓen shugaban ƙasar, lamarin da ya kawo ƙarshen ta'babar da ake yi game da jadawalin gudanar da zaɓuka a ƙasar, wadda ke da mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Shugaban hukumar zaɓen Farfesa Attahiru Jega ya shaidawa taron maneman labarai cewar, a ranar biyu ga watan Afrilun ne kuma za'a gudanar da zaɓukan majalisun dokoki a ƙasar, ya yin da na gwamnoni kuma hukumar ta shiya yin sa a ranar 16 ga watan na Afrilun badin.

Hakanan jadawalin ya tanadi cewar hukumar za ta gudanar da aikin rajistar masu zaɓe ne a tsakanin ranakun 15 da kuma 29 ga watan Janairu, tare da tantance sunayen masu jefa ƙuri'a a tsakanin ranar ukku ga watan Fabrairu da kuma takwas ga watan.

A ƙarƙashin sabon jadawalin dai, hukumar za ta gudanar da zagaye na biyu na zaɓen gwamnoni ko kuma na shugaban ƙasa ne kwanaki bakwai bayan sanar da sakanmakon idan har akwai buƙatar yin hakan.

Jadawalin, ya kuma baiwa jam'iyyun siyasa damar yin zaɓukan fid da gwami a tsakanin ranar 26 ga watan Nuwamba zuwa 15 ga watan Janairu.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Umaru Aliyu