Sabon kundin tsarin mulki a Tunisiya
January 4, 2014Talla
'Yan majalisar dokokin ƙasar Tunisiya sun kaɗa ƙuri'ar amincewa da maida ƙasar a matsayin Jamhuriya ta Musulunci, da ke bin tsarin addinin Islama, amma sun ƙi sa tilas a yi amfani da dokokin Alƙur'ani mai girma, a matsayin dokokin ƙasa. Ƙudurin 'yan majalisa ya ce, Tunisiya ƙasa ce mai 'yancin kai, Jamhuriyar Musulunci. Larabci shi ne harshen da za a riƙa amfani da shi a ayyukan gwamnati, kuma wannan ƙudurin babu mai sauya shi. Ƙasar Tunisiya dai ta kasa samun walwala, tun bayan da aka kifar da gwamnatin kama-karya ta Ben Ali, biyo boren 'yan ƙasar da ya haifar da guguwar juyin-juya hali a wasu ƙasashen Larabawa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammad Nasiru Awal