1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici kan kasafin kudin Najeriya

March 22, 2013

Majalisar Najeriya ta tace bazata amince da sabon kasafin kudin kasar ba, har sai shugaba Goodluck Jonathan tsige shugabar hukumar jarin kasar Oruma Oteh.

https://p.dw.com/p/182tD
©Jonathan Rebboah/Wostok Press/Maxppp France, Paris 25/11/2011 Le president du Nigeria Goodluck Jonathan arrive au palais de l Elysee The President of Nigeria Goodluck Jonathan at the Elysee Palace
Hoto: picture alliance / dpa

Da kyar da gumin goshi dai aka kai ga shawo kan shugaban kasar da ya hau ya kuma yi zaman sa kan kasafin kudin kasar na bana wattani kusan uku bayan mika shi ga fadar tasa.

Babban matsalar dai a tunanin shugaban na zama yin kasafin ba tare da bada kaso ga hukumar kula da hannun jarin kasar ta Najeriya ba sannan kuma da aringizo a cikin kasafin aiyyukan mazabun 'ya'yanta.

To sai dai kuma wata karamar yarjejeniyar da ta tanadi tsara wani karamin kasafin dai ta kai ga shawo kan shugaban da ya amince sannan kuma ya sake mika wani dan karamin kasafin naira miliyan dubu 233 a gaban majalisar domin cika alkawarin ta.

Alkawarin kuma da daga dukkan alamu ke shirin bin shannun sarki bayan da wani zaman majalisar yace sai dai ya tattara nasa ya nasa ya koma kauye ama manta da batun doka in har shugaban kasar ba zai sallami Oteh da ta jawo wani rikicin da ya kai ga gurfanar da shugaban kwamitin kula da kasuwar da mataimakinsa gaban kuliya.

Yan majalisar dai sunce ba batun kasafi ga hukumar in har dai Oteh ce ke zaman shugaba sannan kuma sun zargi shugaba jonsathan da kokarin gwara kansu da yan uwansu na dattawan kasar da suka yi nasarar tabbatar da tilasta shi sauke tsohon shugaban kwamitin fanshon kasar.

The Central Bank of Nigeria was established by the CBN Act of 1958 and commenced operations on July 1, 1959.[1] Governor: Sanusi Lamido Sanusi Headquarters: Abuja, Nigeria Quelle wikipedia, public domain
Babban Bankin Najeriya

Abun kuma da a cewar Hon Ahmed Babba Kaita dake zaman dan majalisar ta wakilai daga Katsina ya sanya daukar matakin nasu ke zaman wajibi a kokarin ceto fadar shugaban kasar daga dauki daidai din da yanzu haka ke barazana ga demokaradiyar kasar.

Kokarin gyara ko ta halin kaka ko kuma neman wani sabon rikici ga kasar ta Najeriya dai rikicin na zaman sabuwar barazana mafi girma ga kasafin da yan kasar ke fatan ganin tasirin sa ga gwamantin dake cikin shekarar ta ta biyu a kan mulki da kuma tuni ta fara fuskantar tambayoyin mu gani a kasa daga talakawan kasar.

Abun kuma da a cewar Auwal Musa Rafsanjani dake zaman shugaban cibiyar kula da harkokin majalisar ya sanya ke zaman kuskure ga yan majalisar da ke ta'allaka matakin nasu kan mutum guda.

Duk da cewar dai a gaba daya sunan uwarsu PDP dangantaka a tsakanin majalisun tarrayar Najeriya biyu da kuma fadar ta shugaba Jonathan dai na kara shiga duhu a wani abun dake iya shafar kokarin alummar kasar na raba tasirin demokaradiya da mulkin soja cikin harkokin rayuwarsu.

( Akwai sautin rahoton daga kasa)

Mawallafi : Ubale Musa
Edita : Zainab Mohammed Abubakar