1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici na shirin barkewa a Mali

October 23, 2013

Hare-haren kunar bakin wake da masu kaifin kishin addini ke kaiwa a Mali na sanya fargabar yiwuwar sake barkewar rikici a kasar.

https://p.dw.com/p/1A5EV
Hoto: Reuters

Tsageru a kasar Mali sun kashe sojojin kasar Chadi biyu tare da wani farar hula guda a wani hari da suka kai , inda wasu sojoji da fararen hula tara suka jikkata a harin da a ka kai din a yankin arewacin kasar Malin da ke fama da rikici.

Harin na wannan Larabar (23.10. 13) dai, na zuwa ne a dai- dai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da bukatar kara yawan sojoji a rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar da ke kasar ta Mali, sakamakon hare-haren makaman roka da na bama-bamai da masu kaifin kishin addini ke ci gaba da kai wa a kan rundunar.

Kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Olivier Salgado, ya bayyana cewa harin, an kaishi ne a wajen binciken ababen hawa a garin Tessalit, da ke gundumar Kidal, wadda ke fama da rikici a arewacin kasar ta Mali.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Saleh Umar Saleh