1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon rikici ya sake ɓarkewa a birnin Mogadishu.

May 18, 2006
https://p.dw.com/p/Buxo

A ƙalla mutane 5 ne rahotanni suka ce sun rasa rayukansu, sakamakon ɓarkewar wani sabon rikici a birnin Mogadishu na ƙasar Somaliya, abin da ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar da aka cim ma, wanda kuma ya fara aiki tun kwanaki 3 da suka wuce.

Rikicin dai ya ɓarke ne yayin da wasu ’yan bindigan ƙungiyoyin islama suka kai wa wani madugun yaƙi hari, a daidai lokacin da ake gudanad da taron kira ga zaman lafiya a birnin, bayan da fafatawar da aka yi a kwanakin baya ya janyo asarar rayukan mutane fiye da ɗari da 40. Dubban jama’a kuma tare da mayaƙan kungiyoyin islama, sun yi ta zanga-zanga a birnin, inda suke Allah wadai da Amirka, suke kuma zarginta da mara wa wasu madugan yaƙin baya.