1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salo a rikicin siyasar Najeriya

April 28, 2014

Gwamnatin tarrayar Najeriya ta janye jami'an tsaron da ke gadin gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako da a makon jiya ya zargi shugaban kasar da zama ummul aba'isin kisan ba gairan dake zaman ruwan dare a arewacin kasar.

https://p.dw.com/p/1BqTB
Murtala Nyako
Hoto: DW/U. Shehu

Ya dai fadi gaskiyarsa komai daci, ya kuma tunkari goshin jirgin dake gudu iya karfinsa, to sai dai kuma tuni ya fara ganin alamun ba dadi ga gwamnan jihar Adamawa Murtala Hammanyero Nyako da rundunar 'yan sandan kasar ta janyewa jami'an tsaron da ke ba shi kariya.

Batutuwan da suka janyo wannan matsalar

Babu dai zato ba kuma tsamanni gwamnan ya aike da wata wasika ya zuwa ga 'yan uwansa gwamnonin arewacin kasar, wasikar kuma da a cikinta yake zargin masu mulkin kasar da zama ummul aba'isin kisan ba gairan da yanzu haka ya mamaye sassa daban daban na arewacin kasar.

Wasikar kuma da ta dauki hankalin kasar tare da tilasta taron daukacin masu ruwa da tsakin kasar da suka zauna da nufin baje ta akan fai fai suka kuma ce sun kare da kama hanya ta gane bakin zare a cikin rikicin da yai sanadiyar halakar yan kasar da daman gaske.

To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai gwamnan da jiharsa ke zaman daya a cikin ukun dake fuskantar dokar ta baci ya fara ganin tasirin bacin ran na Abuja da ta zauna ta zabge masu takama da bashi tsaro na yau da kullum.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria ARCHIV 2013
Shugaba Jonathan na yunkurin shawo kan matsalar tsaron kasarsaHoto: picture-alliance/AP Photo

Daga yansandan ciki dama masu sanye da kayan sarki 173 dake masa gadi dai, Abujar dai ta maida yawan masu tsaron nasa zuwa 30 kacal ga gwamnan da a baya ya kai ga fuskantar barazana ga rayuwarsa.

Hujjojin gwamnati na matakin da aka dauka

Babu dai hujja ko dai daga hedikwatar yan sandan dake nan a Abuja, balle kuma rundunan tsaron cikin gida ta SSS dake da alhakin da samar da tsaron ga manyan mamalakan kasar ta Najeriya.

To sai dai kuma sabon matakin tuni ya fara jawo suka mai zafi daga jami'iyyarsa ta APC dake fadin anyi kure , da kuma a fadar sakatarenta na kasa Tijjani Musah Tumsah ke nuna alamar yanda ake kokari na musgunawa gwamnonin dake fadin gaskiya cikin kasar

“Jihohi na Adamawa da Borno da Yobe cewa akai ana state of emergency, sannan wannan yazo ne bisa ga cewar akwai rashin tsaro, to a cikin rashin tsaron ne ake son a kara rage wa masu kula da tsaro tsaron a wannan jihohi? Basu da wani dalili idan aka ce an rage tsaron ne wa kowane gwamna to da zakace akwai hankali a ciki. Amma wannan abu ne da aka yis hi bisa ga kudurin da aka nufa a zuci . A raunana mai a ci mai fuska a hana shi kudurin da ya ke son ya gudanar.”

Kokari na tsorata masu fadinta komai daci ko kuma rage almubazzaranci da jami'an tsaro dai, da kyar da gumin goshi ne dai Nyakon ya kai ga tsallake rijiya ta bayan baya, sakamakon harin da wasu da ba'a san ko su wanene ba suka kai masa a farkon wannan shekara a jiharsa ta Adamawa.

To sai dai kuma a nata bangaren tuni gwamnatin kekorafin rashin isassu na jami'an tsaron yaki da ta'addanci a kasar, abun kuma ya tilasta jami'an tsaron kasar karin neman dauki da nufin shawo kan matsalar dake neman wucewa da sanin kasar a lokaci kankane.

Nigeria Regierungspartei PDP
Jami'yya mai mulki na fiskantar kalubaleHoto: DW/K. Gänsler

Dr Idi Aliyu Hong dai na zaman tsohon minista a gwamnatin ta Jonathan kuma jigon jam'iyyar PDP a jihar Adamawa, jami'iyar kuma dake zargin gwamna Nyakon da kokari na siyasa da matsalar tsaron dake adabbar yankin na arewa maso gabas

“ Shin me yake so yayi da jami'an tsaro 170 me yake tsarewa ba dan ransa bane ai mutane 30 din sun isa, daga gidansa da ofis da koina wannan duk maganar siyasa ce. Ina jin ko shugaban Amurka ne baya da jami'an tsaro dari da wani abu balle gwamna a Najeriya. Ba wanda yake son tsorata shi. Kundin tsarin mulkin Njeriya ta baiwa kowane dan kasar damar fadin abun da yake ganin kamar da gaskiya”

Abun jira a gani dai na zaman nisan sabon rikicin dake zaman alamu na banbancin dake tsakanin masu ruwa da tsaki da batun tsaron kasar ta Najeriya da kuma ke iya dusashe fata na ganin karshen matsalar a cikin sauri.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Pinado Abdu Waba