1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon salon matakan tsaro a Burundi

Antéditeste Niragira/ Boukari/ LMJuly 22, 2016

Yayin da aka shekara guda da zaben kasar Burundi mai cike da cece-kuce, hukumomin kasar sun farfado da wani salo na samar da tsaro da ya shafi dukkanin manyan biranen kasar.

https://p.dw.com/p/1JUNN
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre NkurunzizaHoto: Getty Images/AFP/F.Guillot

A cikin wannan tsari dai, a kowa ne gida za a sayi wasu kundaye guda biyu wanda a cikinsu kowane mai gida zai rubuta bayannai kan wadanda ke zaune cikin gidan, da kuma duk wata ziyara da wani ya kawo cikin gidan da madalilin kawo ziyarar. Batun kundayen dai batu ne da ya dade ana yinsa a wannan kasa ta Burundi, sai dai a wannan lokaci hukumomin sun kara tsaurara matakin, abun da ya haifar da cece kuce a tsakanin 'yan kasar kuma a cewar François-Xavier matakin ya na da kyau.

Yanayin rayuwa a Bujumbura babban birnin kasar Burundi
Yanayin rayuwa a Bujumbura babban birnin kasar BurundiHoto: DW/K. Tiassou

" Lalle ya kamata cikin kowanne iyali a samu wannan kundi na rubuta bayanai domin a san wadanda suke rayuwa a cikin gidan, kuma idan wani ya kawo ziyara a san dalilin ziyarar tasa."

Kundin na da tsada

Kundi daya dai ana ajiye shi ne ko yaushe a cikin gida, yayin da dayan kuma zai kasance a hannun hukuma. Sannan ana sayan kowanne daya a kudi kimanin 2000 na kasar ta Burundi, farashin da tuni wasu ke ganin tsadarsa. Sai dai a cewar Francois- Xavier, bai kamata a dubi yawan kudi ba, idan har wannan mataki zai kawo inganta tsaro tsakanin al'umma.

Al'umma za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a Burundi
Al'umma za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a BurundiHoto: picture-alliance/dpa/D. Kurokawa

A baya dai ana sayen kundin rubuta bayanan ne a kasuwa, amma kuma yanzu hukumomi suka tilasta sayen wadannan kundaye a hannunta, tare da kara masa kudi. Gabriel Banzawitonde wani manazarcin harkokin yau da kunlum, na ganin cewa wannan mataki na bukatar dubawa ganin halin matsin tattalin arzikin da al'ummar kasar ke ciki.

Yarjejeniya kan sabon salon tsaro

Duk da nuna adawar da wasu 'yan kasar ta Burundi ke yi kan wannan tsari, matakin na daga cikin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin majalisar tsaron kasar ta Burundi da kuma shugabannin kananan hukumomi dan ganin ko wane dan kasa ya kawo tashi gudunmawar a fannin samar da tsaro.